Tinubu Ya Yi Afuwa ga Babban Soja da Aka Kama Ya Sayarwa Ƴan Ta'adda Makamai 7000

Tinubu Ya Yi Afuwa ga Babban Soja da Aka Kama Ya Sayarwa Ƴan Ta'adda Makamai 7000

  • Shugaba Bola Tinubu ya rage wa tsohon jami'in soja, Suleiman Akubo hukuncin daurin rai da rai zuwa shekaru 20 saboda nuna nadama
  • An samu Akubo da wasu sojoji da laifin sayar da makaman gwamnati ga ‘yan tawayen Neja Delta tsakanin 2000 zuwa 2006 a Neja Delta
  • Rahoto ya nuna wasu jami’an tsaro da ‘yan siyasa na cikin masu cin gajiyar ayyukan laifi, musamman satar mai da ake yi a Neja Delta

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Suleiman Alabi Akubo, tsohon babban hafsan rundunar sojin Najeriya, afuwa.

Tinubu ya yi afuwar ne bayan shekaru da dama da yanke wa Akubo hukuncin dauri na rai saboda sayar da makaman soja sama da 7,000 ga tsagerun Neja Delta.

Kara karanta wannan

Atiku ya fusata, ya fadi yadda afuwar Tinubu ta zama barazana ga Najeriya

Tinubu ya yi afuwa ga tsohon babban sojan Najeriya da aka samu da laifin sayar da makamai ga 'yan ta'adda
Shugaba Bola Tinubu ya na rattaba hannu kan wasu takardu gaban shugabannin tsaro. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar.

Tinubu ya yi afuwa ga Manjo Akubo

Suleiman Akubo na cikin jerin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa ko rage masu shekarun hukunci, bayan amincewar majalisar koli a taron majalisar da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja.

Bayo Onanuga ya sanar da cewa, Tinubu ya rage hukuncin Akubo daga daurin rai da rai zuwa zaman gidan yari na shekaru 20 kawai.

Sanarwar ta ce, shugaban kasa ya yi wannan afuwar ne bayan Akubo ya nuna tsantsar nadama da kuma zama mai ladabi bayan yanke masu hukunci.

Akubo, mai shekara 62, ya kasance cikin jerin manyan hafsoshin da aka gurfanar a gaban kotun soja a Kaduna a shekarar 2008.

Kotu ta kuma same su da laifin sayar da makaman gwamnati ga ‘yan tawayen MEND, wanda ke fafutukar kafa kasar Neja Delta.

Kara karanta wannan

Karon farko, yaron Tinubu ya saɓa masa, ya bukaci janye afuwa ga Maryam Sanda

Tarihin laifin da Manjo Akubo ya aikata

Rahoton Reuters ya nuna cewa, tun daga Janairun 2000 zuwa Disambar 2006, Akubo tare da wasu hafsoshin soja sun sace makamai daga manyan dakunan ajiya na rundunar soja dake kwalejin soja ta Jaji da sansanin soja na One Base Ordnance, Kaduna.

Makaman da aka sace sun haɗa da bindigogin AK-47, manyan bindigogi da rokoki, kuma an kiyasta kudinsu a lokacin ya kai Naira miliyan 100.

Bala Usara, alkalin kotun soja a lokacin, ya bayyana cewa masu sayen makaman sun haɗa da Sunny Okah, ɗan’uwan Henry Okah, wanda shi ne shugaban ƙungiyar MEND da ake tuhuma da laifin cin amanar ƙasa da safarar makamai.

A lokacin yanke hukuncin, Janar Emeka Onwamaegbu, kakakin rundunar soja, ya ce:

“Wannan hukunci zai zama darasi ga duk wanda ke shirin bin irin wannan hanya.”
Shugaba Bola Tinubu ya yi afuwa ga hafsan sojan da aka kama da laifin sayar da makamai ga 'yan ta'adda
Shugaba Bola Tinubu ya na rangadi a ranar dimokuradiyya a filin Eagle Square, Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Hannun jami'an tsaro a rikicin Neja Delta

A shekarar 2016, ƙungiyar MEND ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da sake nazarin hukuncin Akubo da wasu sojoji biyar ƙarƙashin shirin afuwar shugaban ƙasa (PAP).

Kara karanta wannan

'Shirin da ake yi na kifar da Tinubu cikin watannin nan idan bai yi hankali ba'

Rahotanni sun nuna cewa tashe-tashen hankula a Neja Delta – wacce ke samar da gangar mai miliyan biyu a rana (a wancan lokaci) sun rage samar da man Najeriya da kashi 20 cikin 100 a farkon shekarar 2006.

Masana tsaro da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce wasu jami’an tsaro da ‘yan siyasa na cikin masu cin gajiyar safarar man da aka yi fasa ƙwaurinsa, abin da ke hana gwamnati kawo ƙarshen matsalar.

Afuwar shugaba kasa: Atiku ya caccaki Bola Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana fargaba a kan yadda Shugaba Bola Tinubu ya yafe wa wasu mutane.

A makon da ya gabata ne, Bola Tinubu ya dauki matakin yi wa wasu mutane 175 afuwa, daga cikin akwai manyan dilolin kwaya da masu kisan kai.

Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce wannan mataki da Tinubu ya dauka daidai ya ke da tauye adalci da nuna iko ta hanyar da ba ta dace ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com