'Yan Sandan Kano Sun Shiga Kaduna, Sun Gano Mabuyar Masu Garkuwa da Mutane

'Yan Sandan Kano Sun Shiga Kaduna, Sun Gano Mabuyar Masu Garkuwa da Mutane

  • Rundunar ’yan sanda ta Kano ta ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kano da Kaduna tsakanin 7 zuwa 9 ga Oktoba, 2025
  • Wani matashi da ya tsere daga hannun masu garkuwa ya taimaka wajen gano maboyarsu a Saya-Saya, karamar hukumar Ikara, Kaduna
  • Kwamishinan 'yan sanda ya ce ba za a bar masu aikata laifi su samu mafaka ba, tare da yabawa jami’an da suka nuna jarumtaka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta samu nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a wasu samame biyu da ta kai.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna kiyawa ya ce an kai samamen ne a Kano da Kaduna, a wani mataki na ƙarfafa yaki da miyagun laifuffuka.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

Rundunar 'yan sandan Kano ta ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da su
Hoton wasu daga cikin jami'an 'yan sandan jihar Kano da suka fito aiki. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

'Yan sandan Kano sun kai samame Kaduna

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ya sanar da cewai, an gudanar da ayyukan ne bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori.

A cewar Kiyawa, an kaddamar da samamen farko a ranar 7 ga Oktoba, 2025, inda sashen yaki da garkuwa da mutane tare da tawagar sa ido ta ofishin ‘yan sanda na Bebeji, suka kai samamen bayan samun sahihin bayanan sirri.

Yadda aka gano maboyar masu garkuwa

Kiyawa ya bayyana cewa an kaddamar da samamen ne bayan wani matashi mai shekaru 21 da aka yi garkuwa da shi, AbdulHamid Bello, ya tsere daga hannun masu garkuwa da shi kuma ya nemi taimako daga jama’a.

Bayan samun bayanansa, ’yan sanda suka bi sawun masu garkuwar zuwa kauyen Saya-Saya a karamar hukumar Ikara, jihar Kaduna, inda suka ceto wani dattijo mai shekaru 65, Musa Idris.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun samu nasara kan mutanen da ake zargi da kisan 'yar jarida a Abuja

“Masu garkuwar sun gudu a lokacin da suka hango jami’an tsaro, suka bar babur da igiya a wajen, wadanda aka kwace a matsayin hujjoji."

- SP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa an mika wadanda aka ceto ga iyalansu bayan sun samu kulawar likita.

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ce masu laifi ba za su samu mafaka a jihar ba.
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori yana jawabi ga manema labarai. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

'Yan sanda sun sake ceto wani saurayi

A wani lamarin na daba da ya faru a ranar 9 ga Oktoba, rundunar ta kuma ceto wani saurayi mai shekaru 19, Ashiru Murtala, wanda aka sace tun ranar 5 ga Oktoba a kauyen Beli, karamar hukumar Rogo ta Kano.

Masu garkuwar sun jefar da shi a cikin wata gonar rake a Hunkuyi da ke Kaduna, bayan da suka hango jami’an tsaro, lamarin da ya sa aka kubutar da shi cikin koshin lafiya.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Bakori, ya ba da umarnin cewa a ba wadanda aka ceto kulawar gaggawa, tare da tabbatar da cewa rundunar ta tsananta bincike don cafke wadanda suka gudu.

An kama masu garkuwa da mutane a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sandan jihar Kano sun ce sun samu gagarumin nasara wajen dakile laifuffuka ta hanyar aikin Operation Kukan Kura.

Kara karanta wannan

Yadda wani 'dan Nijar yake yaudarar mata ya karbi kudi daga hotunan tsiraicinsu

A karkashin wannan aiki, an kama mutane 107 da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban, ciki har da ‘yan fashi, masu safarar miyagun kwayoyi da ‘yan daba.

Rundunar 'yan sandan ta kuma kwato bindigogi, miyagun kwayoyi, motocin sata, babura da kayayyaki masu yawa a cikin watan Agustan 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com