Kano: Ƴan Kwana-Kwana sun ceto dattijo mai shekaru 60 da ya maƙale cikin rijiya

Kano: Ƴan Kwana-Kwana sun ceto dattijo mai shekaru 60 da ya maƙale cikin rijiya

  • Jami'in hukumar kwana-kwana ta jihar Kano sun ceto ran wani dattijo mai shekaru 60 mai suna Adamu Manjo
  • Wani mutum mai suna Abubakar Shehu Musa ne ya dauki hayan Adamu Manjo don ya yashe masa rijiya amma ya makale a ciki
  • Jami'in kwana-kwanan sun turo jami'ansu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru a Danshide Quaters suka ceto Adamu Manjo da ransa da lafiya

Kano - Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ceto wani dattijo mai shekaru 60, Adamu Manjo, da ya makale a cikin rijiya a Danshide Quaters a karamar hukumar Dala na jihar, The Punch ta ruwaito.

Jami'in hulda da mutane na hukumar, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa da aka raba wa manema labarai a ranar Litinin a Kano.

Kara karanta wannan

Lalong ya rufe majalisar jihar Filato don hana tsige shi? Gwamnan ya bayyana gaskiyar lamari

Kano: Ƴan Kwana-Kwana sun ceto dattijo mai shekaru 60 da ya maƙale cikin rijiya
Hoton Rijiya. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

The Punch ta ruwaito cewa Abdullahi ya yi bayani cikin sanarwar cewa lamarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin.

Ya ce:

"Wani Zakari Abdulkadir ne ya kira mu misalin karfe 10.02 na safe kuma nan take muka aike da tawagar mu masu aikin ceto kuma sun isa wurin misalin karfe 10.11 na safe."

Ya ce wani Abubakar Shehu Musa ne ya dauki hayan Manjo ya yashe masa rijiya amma sai ya makale a cikin rijiyar.

Abdullahi ya kara da cewa an ciro leburan daga rijiyar da ransa da lafiyarsa kuma an mika shi hannun wani Alhaji Abubakar Shehu Musa mazaunin Danshide Quarters.

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hoton Mutumin Da Kotu Ta Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Gidan Yari Bayan An Kama Shi Yana Satar Doya

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel