Ana batun Zargin Kisan Kiristoci, Yan Bindiga Sun Yi Ta’asa a Masallacin Katsina
- Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari yayin sallar Asuba a masallaci inda aka samu raunuka
- Maharan sun kai harin ne a masallacin da ke Gidan Lado a karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, inda kwanaki aka yi barna
- Majiyoyi sun tabbatar cewa bayan kai harin, ‘yan ta’addan sun tsere cikin duhu, lamarin da ya jefa al’umma cikin tsoro da tashin hankali
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Malumfashi, Katsina - Duk da sulhu da yan bindiga da ake yi a wasu yankunan jihar Katsina, al'umma na ci gaba da zama cikin fargaba.
Wannan ya biyo bayan ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa a wasu yankunan jihar da ke jawo asarar rayuwa da dukiyoyin al'umma.

Source: Facebook
Rahoton Bakatsine da ke kawo rahoto kan tsaro ya tabbatar a shafin X cewa wasu ‘yan ta’adda dauke da makamai sun kai mummunan hari a cikin masallaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Wannan hari kan masallata na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce a kasa game da zargin kisan kiyashi kan Kiristocin Najeriya.
Wasu mutane daga ketare sun yada cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya wurin amfani da yan ta'adda musamman a Arewa.
Sai dai gwamnatin tarayya, majalisar tarayya, kungiyar Kiristoci ta CAN da wasu daidaikun mutane da masana harkokin tsaro sun karyata jita-jitar.
Lamarin ya jawo maganganu da wasu ke ganin ana neman ta da rigima ne tsakanin Musulumi da Kirista duba da hare-haren sun shafi kowane addini musamman harin da ake kai wa kan masallata.
Yawan hare-hare da ake kai kan masallata a Katsina, Zamfara da Sokoto kadai ba zai lissafu ba tun bayan fara tashin hankali a yankunan.

Source: Original
'Yan bindiga sun kashe mutane a masallaci
Majiyoyin sun tabbatar da cewa maharan sun kai harin ne da sassafe a ranar Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025 din nan da muke ciki.
Lamarin ya faru ne a cikin masallaci yayin sallar Asuba a Gidan Lado a karamar hukumar Malumfashi da ke Jihar Katsina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun kashe mutane biyu cikin masu ibada, tare da jikkata wasu da dama.
Shaidu sun ce maharan sun shigo da bindigogi, suka bude wuta ba tare da tausayi ba, sannan suka tsere bayan sun yi barna.
Legit Hausa ta tattauna da dan Katsina
Muhammad Dahiru ya ce ya tsira daga hannun yan bindiga a ranar Litinin da ta wuce.
Dahiru ya yi magana kan ƙaruwar ta'addanci da ya ke ganin zai yi wahala su iya bari.
Ya ce:
"Matsalar inda take ba za su iya barin ta'addanci ba, amma da za su iya bari yin sulhu shi ne mafi alheri.
"Sun fada mana da kansu gwamnati ce ke yin wannan abin ka ga ba ranar karewarshi kenan."
'Yan bindiga sun sace shugaban majalisar malami
A baya, mun ba ku labarin cewa yan bindiga na ci gaba da kai hare-haren a Arewacin Najeriya wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
An tabbatar da cewa maharan sun tare babbar hanyar birnin Gusau zuwa Gummi a Zamfara da yammacin ranar Talata 7 ga watan Oktobar 2025 da muke ciki inda suka sace malamin Musulunci.
Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun dauki lokaci suna binciken motoci kafin su tafi da mutane zuwa dajin Gummi da ke jihar Zamfara wacce ke fama da matsalolin tsaro a Arewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


