Amupitan: Jam'iyyar ADC Ta Aika Sako ga Sabon Shugaban INEC da Tinubu Ya Nada

Amupitan: Jam'iyyar ADC Ta Aika Sako ga Sabon Shugaban INEC da Tinubu Ya Nada

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC)
  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta yi hannunka mai sanda ga shugaban na INEC biyo bayan nadin da aka yi masa a ranar Alhamis
  • Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa Farfesa Amupitan zai iya sanya sunansa a cikin tarihi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta yi kira da babbar murya ga sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan.

Jam'iyyar APC da bukaci sabon shugaban na INEC da ya nuna aminci ga ‘yan Najeriya, ba wai ga jam’iyyar da ke mulki ba, yayin da yake karɓar ragamar shugabancin hukumar.

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa

ADC ta ba sabon shugaban INEC shawara
Sabon shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da Malam Bolaji Abdullahi. @BolajiADC, @MSIngawa
Source: Twitter

Mai magana da yawun ADC na kasa, Malam Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard ta yi da shi a Abuja ranar Alhamis, 9 ga watan Oktoban 2025.

Me ADC ta ce kan sabon shugaban INEC?

Jam’iyyar ADC ta ce nadin Amupitan ya ba shi damar shiga tarihi a matsayin shugaban INEC da ya gudanar da zaɓe sahihi, nagari, maimakon ya zama dan amshin shatan gwamnati.

Malam Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar na bin al’amuran da taka-tsantsan, ganin cewa har yanzu ba a san sabon shugaban hukumar na INEC sosai ba.

“Har yanzu ba mu san shi sosai ba, saboda haka akwai iyaka ga irin yadda za mu mayar da martani a halin yanzu."

- Malam Bolaji Abdullahi

Wace fata ADC ta yi kan Joash Amupitan?

Sai dai, Bolaji Abdullahi ya bayyana fatan cewa Farfesa Amupitan zai kare mutuncin tsarin zaɓe da kuma yi wa ‘yan kasa adalci.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, Shugaba Tinubu ya gabatar da sunan sabon shugaban INEC na kasa

"Muna fatan zai zama mai aminci ga jama’ar Najeriya, ba ga gwamnati ba. Wannan nadin ya ba shi damar rubuta sunansa cikin tarihi a matsayin shugaban INEC da ya gudanar da zaɓe mai inganci, ba a matsayin abin biyayya ga masu mulki ba. Wannan shi ne ra’ayinmu na farko."

- Malam Bolaji Abdullahi

ADC ta yi martani kan nadin sabon shugaban INEC
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi. Hoto: @BolajiADC
Source: UGC

Jam’iyyar ADC ta kuma ce tsoron da take yi ya yi daidai da damuwar jama’a kan yadda za a kiyaye ‘yancin hukumar INEC.

Ta jaddada cewa wa'adin shugabancin Amupitan zai zama gwajin gaskiya na amincinsa da jajircewarsa wajen kare ka’idojin dimokuraɗiyya.

Kotu ta umarci cafke tsohon shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Osogbo na jihar Osun, ta umarci a cafke tsohon shugaban hukumar INEC.

Kotun ta zargi tsohon shugaban na hukumar INEC da raina ta, saboda haka ta bukaci Sufeton 'yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya cafko Farfesa Mahmood a cikin kwanaki bakwai.

Alkalin kotun, mai shari'a Adefunmilola Demi-Ajayi ta bayar da umarnin ne kafin Farfesa Mahmoud Yakubu ya sauka daga mukaminsa na shugaban INEC bayan kammala wa’adinsa

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng