‘Babban Dalilin da Ya Sa Na Zabi Amupitan, Shugaban INEC’: Tinubu Ya Fadi Hikimarsa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan zabin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC
- Tinubu ya bayyana cewa ya zabi Joash Amupitan ne saboda gaskiyarsa, rashin shigar sa cikin siyasa, da kuma kyakkyawan tarihi
- Farfesa Amupitan shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi da aka taba nada wa mukamin shugaban hukumar ta INEC
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da ya zaba a yau Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025.
Bola Tinubu ya bayyana dalilan da suka sa ya zabi Farfesa Joash Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaben ta INEC.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan bayanai da sadarwa, Bayo Onanuga ya tabbatar a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin sabon shugaban INEC, Farfesa Amupitan
Farfesa Joash Amupitan, mai shekaru 58, haifaffen Ayetoro Gbede ne da ke karamar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.
Kafin wannan nadi, shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (Bangaren Gudanarwa), kuma yana rike da mukamin Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Osun.
Ya karanci ilmin shari’a har zuwa digirin digirgir (PhD) a Jami’ar Jos, bayan ya kammala karatu a Kwalejin Fasaha da ke Ilorin a jihar Kwara.
Baya ga aikin jami’a, Farfesa Amupitan ya taba zama a kwamitocin gwamnati da hukumomi da dama, ciki har da majalisun ilmin shari'a da na malanta wato 'Nigerian Institute of Advanced Legal Studies' da 'Council of Legal Education'.
'Dalilin ba Amupitan shugabancin INEC' - Tinubu
Tinubu ya ce ya nada Amupitan ne saboda rashin nuna bangare a siyasa, gaskiya, da kuma kyakkyawan tarihin aiki da yake da shi.
Shugaban ya ce Farfesa Amupitan shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi da aka taba nada wa wannan mukami mai girma.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a fadar shugaban kasa, Abuja, yayin taron Majalisar Koli ta Kasa da ta amince da nadin Farfesa Amupitan.
An zabi Amupitan ne domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda wa’adin mulkinsa na shekaru goma ya kare a ranar Talata da ta gabata.

Source: Facebook
Tinubu ya jaddada cewa Farfesa Amupitan malami ne na shari’a daga Jihar Kogi kuma mutum ne mai mutunci, wanda ya tabbatar da bin gaskiya da rikon amana a fagen ilimi da shugabanci.
Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Usman Ododo, ya yaba wa nadin, yana mai cewa 'tarihin rayuwar Amupitan ya nuna gaskiya, kishin kasa, da jajircewa wajen hidima ga al’umma.'
Ana sa ran shugaban kasa zai mika sunansa ga majalisar dattawa domin tabbatar da nadin nasa kamar yadda doka ta tanada.
Farfesa Yakubu ya fadi dalilin ajiye aiki
Kun ji cewa Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana dalilin ajiye mukaminsa na shugaban hukumar INEC a Najeriya bayan shafe shekaru 10.
Yakubu ya ce hukumar ta samu cigaba a amfani da fasahar zamani kamar BVAS da bangaren rajista wajen tabbatar da sahihin zabe.
May Agbamuche-Mbu ta karbi ragamar hukumar a matsayin shugabar riko yayin da a yau Alhamis aka nada sabon shugaban hukumar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


