INEC: Yakubu Ya Fadi Dalilin Ajiye Aiki, Tinubu Ya Shirya Nada Magajinsa Makon Nan
- Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana dalilin ajiye mukaminsa na shugaban hukumar INEC a Najeriya bayan shafe shekaru 10 kan kujerar
- Yakubu ya ce hukumar ta samu cigaba a amfani da fasahar zamani kamar BVAS da bangaren rajista wajen tabbatar da sahihin zabe a kasa
- May Agbamuche-Mbu ta karbi ragamar hukumar a matsayin shugabar riko yayin da ake jiran nadin sabon shugaban dindindin a wannan mako
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana dalilin ajiye mukaminsa a hukumar.
Yakubu ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin mukaminsa domin bai wa sabon shugaban damar shigowa da sababbin dabaru wajen gudanar da harkokin hukumar.

Source: Twitter
Yakubu ya fadi cigaban da ya kawowa INEC
A yayin taron da aka gudanar da shugabannin zabe na jihohi (REC) a hedikwatar INEC a Abuja, Yakubu ya mika ragamar ofishin ga May Agbamuche-Mbu, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
May za ta rike mukamin shugabar riko har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban dindindin wanda ake sa Bola Tinubu zai yi a wannan mako.
Yakubu ya ce bayan shekaru 10 a jagorancin hukumar, lokaci ya yi da zai ba wa sabon shugaba damar gyara tsarin zabe, musamman ma wajen shirya zaben 2027 da zabubbukan jihohi.
Ya bayyana cewa hukumar ta samu cigaba sosai a karkashinsa, ciki har da kirkirar tsarin BVAS, inganta rajistar masu kada kuri’a.
A nata jawabin, Agbamuche-Mbu ta gode wa Yakubu bisa irin jagoranci da tsari da ya kafa a hukumar INEC, tare da alkawarin kiyaye mutuncin hukumar da kuma ci gaba da aiki da sahihanci da gaskiya.

Source: Facebook
Yaushe Tinubu zai 'nada' sabon shugaban INEC
Rahotanni sun bayyana cewa, Shugaba Tinubu zai sanar da sabon shugaban INEC bayan taron Majalisar Koli ta Kasa da za a yi a Abuja a gobe Alhamis, inda zai gabatar da sunayen masu neman mukamin.
Rahoton Vanguard ya ce a halin yanzu, May Agbamuche-Mbu wacce lauya ce kuma kwararriya a harkar shari’a, ta karbi mukamin shugabar riko har sai an nada sabon shugaban na dindindin.
Farfesa Yakubu, wanda aka nada a karo na farko a 2015, ya gudanar da manyan zabubbuka na 2019 da 2023, inda ya kawo tsarin mafani da na’urorin BVAS da 'Rukunin kallon sakamakon zabe (IReV)', wadanda suka kawo sauyi.
Duk da cewa an samu matsalolin fasaha da jinkiri a wasu lokuta, Yakubu ya samu yabo wajen kare 'yancin hukumar INEC daga matsin lamba na siyasa da kuma dorewar tsari mai zaman kansa.
Tinubu ya karrama Farfesa Yakubu da lambar yabo
Kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya magantu da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aiki bayan shafe shekaru 10.
Tinubu ya amince da barin Farfesa Yakubu mukamin shugaban hukumar INEC bayan karewar wa’adinsa na biyu tun da ya hau kujerar a 2015.
Shugaban ya yaba da jajircewar Yakubu wajen gudanar da zabubbuka masu tsafta tare da ba shi lambar yabo ta CON saboda hidimarsa ga kasa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

