Magana Ta Kare, Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Sunan Sabon Shugaban INEC na Kasa

Magana Ta Kare, Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Sunan Sabon Shugaban INEC na Kasa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin shugaban hukumar zabe (INEC)
  • Tinubu ya gabatar da sunan Amupitan a taron Majalisar Magabata ta Kasa kuma sun amince da shi yau Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025
  • Farfesa Amupitan masanin doka ne wanda ya dade yana aikin koyarwa a Jami'ar Jos kafin ya zama Mataimakin Shugaban Jami'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Majalisar Magabata ta Ƙasa ta amince da naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga yankin Arewa ta Tsakiya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan ga majalisar domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya kammala wa'adinsa na shekara 10.

Kara karanta wannan

Amupitan: Jam'iyyar ADC ta aika sako ga sabon shugaban INEC da Tinubu ya nada

Shugaban INEC mai jiran gado, Farfesa Amupitan.
Hoton shugaban hukumar INEC mai jiran gado, Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN). Hoto: Joash Ojo Amupitan (SAN)
Source: Facebook

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Alhamis.

Tinubu ya fadi dalilin nada Amupitan

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Farfesa Amupitan shi ne mutum na farko daga jihar Kogi a yankin Arewa ta Tsakiya da aka zaɓa don rike wannan mukami, kuma ba ya da alaka da kowace jam’iyya ta siyasa.

Mambobin Majalisar Magabata gaba daya sun amince da naɗin Amupitan, inda Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana Farfesan a matsayin mutum mai gaskiya da amana.

A cewar Shugaban Ƙasa, za a aika da sunan Farfesa Amupitan zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa kamar yadda doka ta tanada.

Takaitattun bayanai game da Amupitan

Farfesa Amupitan, mai shekara 58, ɗan asalin kauyen Ayetoro Gbede a ƙaramar hukumar Ijumu ta Jihar Kogi ne. Shi malami ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, kuma tsohon ɗalibin jami’ar.

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa

Yana da ƙwarewa a fannonin Dokar Kamfanoni, Shaidar Shari’a, da Gudanar da Kamfanoni, ya zama babban lauya a Najeriya watau SAN a watan Satumba, 2014.

An haifi Farfesa Amupitan a 25 ga Afrilu, 1967. Bayan kammala makarantar firamare da sakandare, ya halarci Kwalejin Fasaha ta Kwara da ke Ilorin (1982–1984).

Farfesa Amupitan.
Hoton shugaban INEC mai jiran gado, Farfesa Amupitan da Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daga nan ya wuce Jami’ar Jos, ya karanci kwas din Lauya daga 1984 zuwa 1987), sannan ya karbi rantsuwar zama cikakken lauya a 1988. Ya yi bautar kasa (NYSC) a Bauchi.

Ya samu LL.M daga Jami’ar Jos a 1993 da kuma Digirin PhD a 2007, bayan fara aikin koyarwa tun daga 1989, cewar rahoton Daily Trust.

Yanzu haka, Amupitan ke rike da kujerar Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (bangaren gudanarwa) kuma shi ne Shugaban Majalisar Gudanarwa ta Jami'ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun kafin wannan nadin.

ADC ta ja hankalin sabon shugaban INEC

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ja hankalin sabon shugaban INEC, Farfesa J. Amupitan da ya kasance mutum mai gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Ana sa ran Tinubu ya fadi sabon shugaban INEC a zaman majalisar koli

ADC, jam'iyyar da jagororin adawa suka yi hadaka domin kayar da gwamnatin APC, ta tunawa Amupitan cewa Najeriya zai yi wa aiki ba wata jam'iyya ba.

Jam'iyyar ta ce wannam nadi ya ba Amupitan wata damar shiga tarihi a matsayin shugaban INEC idan ya gudanar da zaɓe sahihi, wanda kowa zai yi na'am da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262