Jami'an Tsaro Sun Cafke Barawon da Ya Sato Motar Asibiti daga Kasar Nijar

Jami'an Tsaro Sun Cafke Barawon da Ya Sato Motar Asibiti daga Kasar Nijar

  • Dubun wani barawon mota ta cika bayan jami'an hukumar shige da fice ta kasa (NIS) sun yi caraf da shi a jihar Jigawa
  • Jami'an na hukumar NIS sun cafke barawon ne bisa zargin sato wata motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya
  • Dubun barawon ta cika ne bayan ya shigo da motar asibitin zuwa iyakar Najeriya da Nijar, inda jami'an tsaro suka yi caraf da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Jami’an hukumar shige da fice ta kasa (NIS) reshen jihar Jigawa, sun samu nasarar cafke wani matashi bisa zargin sata.

Jami'an na hukumar NIS a Jigawa sun cafke matashin ne bisa zargin sato wata motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Najeriya.

Barawon mota ya shiga hannun jami'an tsaro a Jigawa
Sufeto Janar na 'yan sanda, Kayode Egbetokun da shugabar hukumar NIS, Kemi Nandep. Hoto: @nigimmigration, @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta kawo rahoton cewa shugaban hukumar NIS na jihar Jigawa, Tahir Abdullahi Musa, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Kano: 'Dan jarida ya debo ruwan dafa kansa, ICPC ta kama shi kan zambar N14m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka cafke barawon motar asibiti

Jami'an tsaron sun cafke matashin ne yayin da yake kokarin shigo da motar asibitin da ake zargin ya sato daga Jamhuriyar Nijar, zuwa Najeriya.

Shugaban na hukumar NIS ya bayyana sunan matashin da aka cafke a matsayin Yusif Bashir.

Tahir Abdullahi Musa ya ce an kama wanda ake zargin da motar asibiti kirar Toyota Land Cruiser mai lamba ONG-0777, bayan ya samu nasarar shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar.

Wane mataki hukumar NIS za ta dauka?

Shugaban na NIS ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen sada shi da rundunar ’yan sandan jihar Jigawa.

Ya ce za a mika wanda ake zargin ne zuwa ga hannun 'yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.

Hakazalika ya kara da cewa hukumar NIS za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban majalisa ya ceto shugaban marasa rinjaye daga yunkurin tsige shi

Dubun barawon mota ta cika a Jigawa
Taswirar jihar Jigawa, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan hukumar shiga da fice

An kai jami'in hukumar NIS kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta gurfanar da wani jami'in hukumar shige da fice ta kasa (NIS,), bisa zargin rashin gaskiya.

Ana zargin jam'in na hukumar NIS da karbar albashin da ya kai N17.6m daga wasu hukumomin gwamnati guda uku.

Hukumar ICPC ta kai Abubakar Mohammed Aseku gaban kotu bisa zargin cewa ya karbi albashin N17.6m daga ma’aikatu daban-daban a wani tsawon lokaci, lamarin da ya sabawa dokokin aikin gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng