Kano: 'Dan Jarida Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, ICPC Ta Kama Shi kan Zambar N14m
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya ta bayyana cewa wani 'dan jarida, mai suna Alkazim Kabir ya shigo hannunta
- Tana shirin gurfanar da shi a gaban kotu bayan an same shi da hannu a cikin damfara, karya da handame kudin jama'a da ya kai N14m
- ICPC ta bayyana cewa Alkazim na amfani da dabaru daban-daban wajen damfarar, ko rancen makudan kudin kasar waje daga bayin Allah
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bayyana shirin gurfanar da wani mutum mai suna Alkazim Kabir a gaban kotu.
Alkazim, wanda aka fi sani da Abbati Kabiru Abuwa, wanda ke ikirarin cewa shi ɗan jarida ne a jihar Kano, ya shiga hannu a kan zargin damfara da ya kai kimanin Naira miliyan 14.

Kara karanta wannan
Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Demola Bakare, ya fitar a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ICPC ta kama 'dan jarida a Kano
Daily post ta wallafa cewa ICPC ta yanke shawarar gurfanar da Kabir ne bayan samun korafe-korafe da dama kan yadda ya rika damfarar mutane.
Wasu daga cikin hanyoyin da ya ke bi wajen yin zamba da damfara sun hada da kwaikwayon jami’an gwamnati da bayyana kansa a matsayin wakilin gwamnati.
Binciken hukumar ICPC ya gano cewa Alkazim ya rika kwaikwayon hadiman Shugaban Kasa da Mataimakinsa, da kuma wasu 'yan Majalisar Tarayya domin damfarar bayin Allah.
A wani misali, an ce ya karɓi $3,300 da kuma riyal 1,620 daga wasu mutane biyu, yana ikirarin cewa shi wakili ne na Shugaban Ƙasa da Mataimakinsa.
Idan aka yi lissafi a farashin kasuwar canji a yau, wadannan kudi kawai sun zarce N40m.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Za a rika biya wa talabijin da radiyo haraji, jama'a sun fara korafi
Ana zargin 'dan jaridan Kano da damfara
Bakare ya bayyana cewa bincike ya ƙara nuna yadda 'dan jaridan ya fi amfani da damar da ke da alaƙa da addini kamar hajji da umrah domin zambatar jama'a.

Source: Original
Haka zalika, ya aika takarda na bogi da ta nuna cewa ya biya Naira miliyan 3.2 ga wani dillalin tafiye-tafiye da ya taimaka masa wajen shirya jirgi, otal da jirgin kasa.
ICPC ta yi nasara kan gwamnatin Kano
A baya, mun wallafa cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin mai shari’a Josephine Obanor, ta ƙi yarda da ƙorafin da gwamnatin jihar Kano ta shigar a kan ICPC.
Wasu jami'an gwamnati sun shigar da kara, suna neman a hana Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) gudanar da bincike kan zargin almundahana a tsarin tallafin karatu a jihar.
Kotun ta tabbatar da cewa ICPC na da hurumin bincike bisa doka, kuma gayyatar da ta yi wa ma’aikatan jihar ba za ta iya zama tauye haƙƙin ɗan adam ba kamar yadda aka shigar gabanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng