UNICEF: Yadda Najeriya Ta Yi Asarar Dala Biliyan 10 a Bauchi da Jihohin Arewa 5
- Hukumar UNICEF ta ce Najeriya ta yi asarar dala biliyan 10 sakamakon rikicin Boko Haram na fiye da shekaru 10 a Arewa maso Gabas
- Shirin UNICEF zai horar da yara fiye da 1,000 kowace shekara kan sana’o’i kamar ICT, dinki, gyaran mota da kafinta a jihar Borno
- Gwamnatin Borno ta gode wa UNICEF da kungiyoyi uku bisa kokarin dawo da yara cikin al’umma bayan shafe shekaru cikin rikici
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno – Hukumar UNICEF ta bayyana cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10 sakamakon rikicin fiye da shekaru 10 a yankin Arewa maso Gabas.
UNICEF ta sanar da hakan ne a ranar Laraba a Maiduguri, yayin ƙaddamar da wani shiri na dawo da yaran da rikicin ya shafa cikin al’umma.

Source: Twitter
Rahoton The Punch ya nuna cewa an kaddamar da shirin domin taimaka wa waɗanda suka tsinci kansu cikin wahala saboda tasirin yaƙin Boko Haram.
Asarar $10bn a jihohin Arewa maso Gabas
Wakiliyar UNICEF ta kasa a Najeriya, Wafaa Saeed, ta ce binciken da hukumar ta gudanar a 2024 ya nuna cewa rikicin Arewa maso Gabas ya jawo Najeriya ta yi asarar dala biliyan 10 a cikin shekaru 10.
Wafaa Saeed, wacce Shah Mohammad Khan, shugaban sashen kare yara na UNICEF, ya wakilta, ta bayyana cewa rikicin bai tsaya ga lalata tattalin arziki na ƙasar kawai ba.
Ta bayyana cewa rikicin ya rusa rayuwar jama’a da kuma ƙarfin samun kuɗin shiga musamman a tsakanin iyalai da matasa marasa ƙarfi.
Ta ce,
“Rikici ya raunana tattalin arzikin Najeriya, ya durƙusar da samun kuɗin shiga na iyalai da matasa. Shekaru da dama yara da samari, musamman ’yan mata suna rasa damar koyon sana’a ko cimma burinsu.”
Rikicin ya fi shafar yara da mata a Arewa
Wafaa Saeed ta nuna damuwarta cewa rikicin da ya daɗe a yankin ya haifar da mummunan cin zarafi ga yara, ciki har da sace-sace, fyade da lalatawa, tare da rasa hanyoyin dogaro da kai.
Ta ce wannan matsala ta yi mummunar illa ga ci gaban ɗan adam da karuwar ilimi da sana’a a yankin, musamman a tsakanin yara masu tasowo.
UNICEF ta ƙaddamar da sabon shirin SERP domin taimaka wa yaran da rikici ya shafa ta hanyar horar da su da sana’o’in dogaro da kai da sauransu.
A halin yanzu, yara 1,033 (maza 567 da mata 466) suna cin gajiyar wannan shiri a cibiyoyi daban-daban da ke Maiduguri, Bama, Biu, Damboa, da Konduga.
Wafaa Saeed ta bayyana cewa ana koyar da yaran sana’o’i kamar dinkin kaya, gyaran mota, ICT, yin takalma da kafinta da sauran su, inji rahoton PM News.
“Wannan horo ba kawai koyarwa ba ne, amma hanya ce ta dawo da karsashi, mutunci da damar fara sabuwar rayuwa ga yaran da rikici ya shafa.
- Abba Wakilbe.

Source: Facebook
Gwamnatin Borno ta yaba da taimakon UNICEF
UNICEF ta ce ana sa ran fiye da yara 1,000 za su ci gajiyar wannan shiri a kowace shekara, inda za su samu sana’o’in da za su iya dogaro da kansu da kuma samun aikin yi a nan gaba.
Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na Borno, Abba Wakilbe, ya yaba da aikin UNICEF da abokan haɗin gwiwarta — UNDP, IOM da UNODC — bisa tallafin da suke bai wa jihar domin farfaɗo da rayuwar yaran da rikici ya shafa.
“Muna godiya ga UNICEF saboda taimako mai yawa da suke yi mana, musamman a lokutan da muka fi buƙatar su.”
- Abba Wakilbe.
Mutane miliyan 139 na rayuwa a talauci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Bankin Duniya ya ce mutane miliyan 139 ke rayuwa cikin talauci a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziki.
Bankin ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan cire tallafin mai da sauyin musayar kudi, amma ya nemi gwamnati ta maida hankali kan rayuwar talakawa.
An kuma gargadi shugaban kasar cewa cewa hauhawar farashin kaya musamman abinci na iya kawo barazana ga ci gaban sauye-sauyen gwamnati
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



