Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas

Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas

  • UNICEF ta bayyana cewa a kalla rayukan yara 300,000 aka rasa sakamakon ta'addancin Boko Haram a arewa maso gabas ta Najeriya
  • Kamar yadda kiyasin ya bayyana, a cikin shekaru 12 da suka gabata ne gobara, bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki yayi ajalin yaran
  • A kalla yara 5,129 ne suka bar makaranta saboda matsalar lafiyar kwakwalwa da suke fama da ita sakamakon rikicin da arewaci ya fada

Sama da yara 300,000 ne suka rasa rayukansu a shekaru 12 da suka gabata sakamakon ta'addancin da ya addabi yankin arewa maso gabas, kiyasin kwanakin nan da UNICEF ta saki ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin Najeriya sun bayyana cewa ISWAP ta fara gangamin daukan matasa marasa aikin yi aiki domin tada zaune tsaye, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwastam za ta fara amfani da 'Drone' wajen sintiri da kama haramtattun kayayyaki

Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas
Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Kiyasin kwanan nan da UNICEF ta saki ya kara da bayyana cewa sama da mutum miliyan daya sun rasa gidajensu a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Rahoton ya ce a kalla yara 5,129 ne suka bar makaranta sakamakon kalubalen matsalar lafiyar kwakwalwa da suke fama da ita sakamakon rikicin da arewaci ya fada.

A yayin da Daily Trust ta nemi samun karin bayani kan abubuwan da suka zama sanadin mutuwar yaran 300,000, UNICEF ta ce an tattaro kiyasin ne ta hanyar tattara jimillar yaran da suka rasu kai tsaye da wadanda ba kai tsaye ba yayin farmakin.

Ya ce:

"Yara sun rasa rayukansu sakamakon gobara, tashin bama-bamai, rashin abinci mai inganci da sauransu."

Salihu Bakhari, wanda jami'in tsaro ne da yayi murabus, ya ce bai yi mamakin wannan kiyasi da UNICEF ta saki ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

"Yanzu ne muka fara bayyana gaskiya saboda hankalinmu ya fara dawowa kan farmaki da barnar da ake mana. Ba mu mayar da hankali kan irin abubuwan da ke faruwa ba kuma ya ke ritsawa da yara.
"Na tabbatar da cewa nan babu dadewa a watanni masu zuwa za a sake samun wasu amma mafi amfani kuma mafi dacewa shi ne masu ruwa da tsaki su fara tunanin yadda za su shawo kan wannan kalubalen.
"Akwai yara da yawa da suka bace, wasu an sace su kuma wasu na hannun 'yan ta'adda. Suna rainonsu tare da koya musu yadda za su zama mayakan ta'addanci.
"Toh a yayin da muke Allah wadai tare da koka wa kan kisan 'ya'yanmu, dole ne mu kara zagewa domin ceto wadanda ke hannun miyagun kuma a sa rayuwarsu ta zama mai amfani," yace.

Kaduna: Hotunan 'yan sanda masu murabus suna yi wa hukumar fansho zanga-zanga

A wani labari na daban, 'yan sandan da suka yi murabus sun fita zanga-zangar lumana kan rike musu kudade da hukumar fansho ta jihar Kaduna ta yi a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun fara gangamin diban jama'a aiki, Rundunar sojin kasa

Jami'an sun yi tattaki har zuwa hedkwatar rundunar 'yan sandan jihar Kaduna domin mika kokensu inda suka jaddada cewa ba su da ra'ayin abinda suka kwatanta da "hukumar kisa".

A na tsawon wani lokaci, jami'an 'yan sanda a kasar nan suna ta kushe hukumar fansho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng