Ministan Tinubu da ake zargi da Takardun Bogi Ya Fadi Dalilinsa na Ajiye Aiki
- Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-kirkire, Uche Nnaji da ya yi murabus daga mukaminsa ya kore shakku a kan dalilin ajiye aiki
- A makon da ya gabata ne aka fitar da rahoto da ke nuna cewa Nnaji na amfani da takardun kammala karatu na bogi daga jami'ar UNN
- Kuma jami'ar ta tabbatar da labarin, inda ta ce Uche Geoffrey Nnaji ba shi daga cikin wadanda su ka kammala karatu daga jami'ar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Tsohon Ministan Kimiyya, Fasaha da Kirkire-Kirkire na Najeriya, Uche Geoffrey Nnaji, ya bayyana ainihin abin da ya jawo aya yi murabus daga mukaminsa.
Ya ce barin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi ba ya nufin ya amsa zargin da ake yi masa na amfani da takardun karatun bogi da aka yi zarginsa da shi.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa tsohon Ministan na wannan ikirari ne duk da cewa an samu hujjoji masu ƙarfi da ke nuna cewa ya gabatar da takardun karatu na ga gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Tinubu ya ajiye mukaminsa
Daily Trust ta wallafa. Da Nnaji ya ajiye mukaminsa ne ranar Talata bayan wani bincike da ya bayyana cewa ya ƙirƙiri takardar kammala karatu daga Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), da kuma takardar NYSC.
A wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Talata, Nnaji ya ce:
"Yanke shawarar ajiye mukamina abu ne da na yi da zuciya ɗaya. Ba wai amsa laifi ba ne, illa dai na yi hakan ne don mutunta tsarin shari’a da kuma kare mutuncin kotu da ke sauraron shari’ar."
A cewarsa, murabus ɗin nasa hanya ce da zai ba wa gwamnati damar ci gaba da aiki ba tare da wata tangarda daga matsalolinsa na kashin kai ba.

Kara karanta wannan
Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki
Tsohon ministan kimiyyar ya soki gidan jarida
Duk da hujjojin da suka fito daga UNN da hukumar NYSC waɗanda suka musanta cewa sun fitar da takardun da Nnaji ya gabatar, tsohon ministan ya zargi Premium Times da yarfe.
Nnaji ya kara da cewa wannan ya fara janyo masa damuwa da kuma rikita aikin ma’aikatarsa da manufofin Shugaban Kasa na cicciba Najeriya.

Source: Facebook
A yayin da ya ke ƙoƙarin kare kansa, an gano cewa Nnaji ya shigar da ƙara kotu yana ƙoƙarin hana jami’ar UNN da Ma’aikatar Ilimi fitar da bayanan karatunsa zuwa ga manema labarai.
Atiku na son a binciki Tinubu da ministocinsa
A baya, mun wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa murabus ɗin Uche Nnaji daga matsayin Ministan Kimiyya da Fasaha rufa-rufa ce.
A cikin sanarwar, Atiku ya ce bai kamata a bar Nnaji yana murabus ba tare da a gurfanar da shi a gaban kotu ba, domin wannan hanya ta nuna cewa gwamnati ba ta ɗaukar laifi da muhimmanci.
Atiku ya jaddada cewa idan gwamnati ta yi watsi da wannan lamari, to zai zama alamar cewa ana ɗaukar bogi da yaudara a matsayin abin alfahari a cikin shugabancin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

