Amupitan: Farfesa daga Jami'ar Jos na Dab da Zama Sabon Shugaban Hukumar INEC
- Wa’adin shekaru 10 na Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban INEC ya kare a ranar Talata, 7 ga watan Agusta, 2025
- Rahotanni sun nuna cewa Farfesa Joash Ojo Amupitan ne ke kan gaba cikin jerin wadanda ake sa ran za su maye gurbin Yakubu
- Ana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai sanar da sunan sabon shugaban INEC bayan taron majalisar koli ta kasa a ranar Alhamis
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tsawon shekaru 10, kuma ya kammala wa’adinsa a ranar Talata.
Bayan sauka da mulki, ya mika ragamar ofishinsa ga Mrs. May Agbamuche-Mbu, daya daga cikin kwamishinoni na kasa a hukumar, a matsayin shugabar riko.

Source: UGC
Shugaban INEC, Yakubu ya ajiye aiki
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Yakubu ya mika ragamar ne bayan taron da ya gudanar da kwamishinonin zabe (RECs) a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Na yanke shawarar sauka daga kan mukamina kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya, Sashe na 36, ya tanada.
"Ajiye aikin tun a wannan lokaci zai ba wanda zai gaje ni damar fara shirye-shiryen zabe cikin nutsuwa."
- Farfesa Mahmood Yakubu.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon shugaban INEC ya yi niyyar ajiye mukaminsa tun watan Yuni, amma aka shawarce shi da ya ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen wa’adinsa.
INEC: Tinubu zai gabatar da magajin Yakubu
Majiyar jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da sunan wanda ya zaba a matsayin sabon shugabar INEC ga mambobin majalisar koli ta kasa.
An rahoto cewa majalisar koli ta kasa za ta gudanar da zamanta ne a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis mai zuwa.
Bayan taron ne ake sa ran jin sunan wanda aka zaba a matsayin magajin Farfesa Mahmood Yakubu, kuma wanda zai jagoranci zabuka masu zuwa.
Joash Amupitan na iya zama shugaban INEC
Daga cikin wadanda ake tunanin za su gaji Farfesa Yakubu, rahotanni sun nuna cewa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) ne ke kan gaba a jerin.

Source: Twitter
Farfesa Amupitan shi ne mataimakin shugaban jami’ar Jos (bangaren gudanarwa), kuma fitaccen masanin doka.
An haifi Farfesa Amupitan a ranar 25 ga Afrilu, 1967, a Aiyetoro-Gbede, karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi.
Ya shafe shekaru da dama yana koyar da shari'a a jami’a tare da taka muhimmiyar rawa a fannin gyaran tsarin doka da shugabanci a Najeriya.
Da aka tuntubi kwamishinan yada labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, kan rahoton cewa ɗan jihar Kogi ke kan gaba don zama shugaban INEC, sai ya ƙi yin tsokaci, yana mai cewa ba shi da izinin magana kan batun.
Abin da Yakubu ya fadawa Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mahmood Yakubu ya miƙa wa shugaban ƙasa Bola Tinubu takardar ajiye aikinsa a hukumance ranar 3, Oktoba, 2025.
A cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban ƙasa Tinubu, Yakubu ya bayyana godiyarsa bisa damar da aka ba shi ta yin hidima ga ƙasa.
Farfesa Mahmood Yakubu ya roƙi a amince da murabus ɗinsa daga ranar Talata, 7, Oktoba, kafin karewar wa’adin aikinsa a watan Nuwamba, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


