AfDB: Tinubu Zai Karbi Sabon Rancen Naira Biliyan 733, za a Yi Aiki a Bangarori 3
- Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) ya sanar da shirinsa na sake ba Najeriya rancen dala miliyan 500 kafin ƙarshen 2025
- Wannan na cikin rancen tallafin kasafin kuɗi na dala biliyan 1 domin rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki a Najeriya
- Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya fadi manyan bangarori uku da za a kashe wa $500m din
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Babban Bankin Raya Afirka (AfDB) ya bayyana shirinsa na fitar da dala miliyan 500 ga Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2025.
Za a fitar da kudin ne a matsayin kashi na biyu na tallafin bashin kasafin kuɗi na dala biliyan 1 da aka tsara domin tallafawa sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu.

Source: Twitter
Bankin AfDB zai ba Najeriya rancen $500m

Kara karanta wannan
Mutane za su amfana da Najeriya ta fara shirin karbo bashin tiriliyoyin Naira daga China
Dr. Bode Oyetunde, wakilin Najeriya da São Tomé and Príncipe a AfDB ne ya tabbatar da hakan a gefen taron tattalin arzikin Najeriya na 31 da ake gudanarwa a Abuja, inji rahoton Finance in Africa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun kuduri niyyar tallafawa sauye-sauye masu karfi da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa yanzu.
"Wannan tallafi na da matukar muhimmanci wajen taimakawa Najeriya ta magance kalubalen tattalin arziki da take fuskanta."
- Dr. Bode Oyetunde.
Amfanin rancen $500m ga Najeriya
Dr. Oyetunde ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta nemi rancen dala biliyan 1.5, amma bankin ya amince da rancen dala biliyan 1 kawai.
Wannan rancen, za a raba shi cikin shekaru biyu – dala miliyan 500 a 2024, da sauran dala miliyan 500 a 2025 bayan amincewar hukumar gudanarwar bankin.
Ya ce ranen zai taimaka wajen daidaita tsarin kuɗi, gyaran sashen wutar lantarki, da inganta tsarin gudanarwa na gwamnatin tarayya.
Wakilin AfDB ya kuma ce yarda cewa sauye-sauyen gwamnatin Tinubu "sun rikita tattalin arziki,” amma ya ce suna da muhimmanci domin dawo da kwarin gwiwar masu zuba jari da ci gaba mai dorewa.
A Nuwambar 2023, ministan kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da rancen dala biliyan 1 daga AfDB domin tallafawa kasafin kuɗi da aiwatar da gyare-gyare.
Gwamnati za ta yi amfani da dala miliyan 500 da AfDB zai fitar kafin ƙarshen 2025 wajen gyaran harkar wutar lantarki, bunkasa aikin noma, da daidaita tsarin kuɗi.

Source: Twitter
Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu
The Punch ta rahoto cewa, tun bayan hawansa mulki a watan Mayu 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da jerin sauye-sauyen tattalin arziki da suka hada da:
- Cire tallafin man fetur da aka dade ana bayarwa
- Dunkule farashin musayar kudi daga kasuwanni da dama zuwa wuri daya
- Sababbin dokokin haraji da kasafin kuɗi domin farfado da tattalin arzikin ƙasa
A cewar Oyetunde, AfDB ta dauki wannan mataki ne don taimakawa Najeriya ta daidaita kasafin kuɗi da rage tasirin hauhawar farashi bayan rikicin tattalin arzikin duniya da rikicin bayan COVID-19.
Najeriya ta karbi rancen dala miliyan 250
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Bankin Duniya ya ƙara sakin Dala miliyan 215 domin shirin bayar da tallafin kuɗi ga 'yan Najeriya.
Jimillar kuɗin da aka riga aka saki yanzu ya kai Dala miliyan 530 daga cikin Dala miliyan 800 da aka amince da su a baya.
Bayanai sun nuna cewa ana biyan gidaje miliyan 15 tallafin N25,000 na wata-wata tsawon wata uku karkashin wannan sabon tsari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

