Ministan Tinubu da Ake Zargi da Jabun Takardu Ya Hakura da Kujera, Ya Yi Murabus

Ministan Tinubu da Ake Zargi da Jabun Takardu Ya Hakura da Kujera, Ya Yi Murabus

  • Ministan kimiyya, kirkire-kirkire da fasaha na Najeriya, Geoffrey Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukamin da yake kai
  • Rahotanni sun bayyana cewa Geoffrey Uche Nnaji ya ajiye aiki ne bayan zarginsa da ake yi da yin jabun takardu guda biyu
  • Yayin da Shugaba Bola Tinubu ya karɓi murabus ɗinsa, Nnaji ya ce yana fuskantar batanci sosai daga abokan adawar siyasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha na ƙasa, Geoffrey Uche Nnaji, ya yi murabus daga mukaminsa.

Murabus din Minista Geoffrey Uche Nnaji ta na zuwa ne bayan wani rahoto da ya bayyana cewa ya na amfani da takardun bogi guda biyu.

Ministan kimiyya da fasaha, Geoffrey Nnaji ya yi murabus daga mukaminsa
Hoton Shugaba Bola Tinubu da na tsohon ministan kimiyya da fasaha Geoffrey Nnaji. Hoto: @officialABAT, @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Ministan kimiyya, Geoffrey Nnaji ya yi murabus

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (tsohuwar Twitter) a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: An nemi Ministan Tinubu ya yi murabus, ya mika kansa ga hukuma

A cewar sanarwar:

“Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi murabus ɗin Geoffrey Uche Nnaji, ministan kirkire-kirkire, kimiyya da fasaha, bayan zarge-zargen da ake yi masa.
"Shugaban ƙasa ya nada Nnaji a watan Agusta 2023.
"Ya yi murabus yau ta hanyar wasikar da ya aika (wa gwamnati) inda ya gode wa shugaban ƙasa bisa damar da ya ba shi ta yi wa Najeriya hidima.”

Nnaji ya koka da batanci daga abokan adawa

A cikin wasikar murabus ɗinsa, Minista Uche Nnaji ya ce ya zama abin batanci da farfaganda daga abokan adawar siyasa, yana mai cewa ba zai iya jure wannan matsin lamba ba.

“Na gode wa shugaban ƙasa saboda damar da ya ba ni, amma matsin lambar siyasa da batanci sun yi yawa. Don haka, ina ganin ya dace in sauka domin kada wannan rikici ya shafi gwamnati."

- Geoffrey Uche Nnaji.

Tinubu ya yi godiya ga tsohon ministan

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya karɓi murabus ɗin Nnaji, yana mai gode masa bisa “lokacin da ya bayar wajen hidimtawa ƙasa."

Shugaban kasar ya kuma yi wa tsohon ministan fatan alheri a ayyukansa na gaba, yayin da ya yi bankwana da majalisar zartarwa ta kasa.

Wannan murabus din na zuwa ne yayin da ake ci gaba da bincike kan zargin amfani da takardun makaranta da na NYSC na bogi da tsohon ministan ya yi.

Shugaba Bola Tinubu ya yi godiya ga ministan kimiyya da ya yi murabus bisa hidimtawa kasa
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a wani taro a birnin tarayya Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Zarge-zargen da ake yi wa minista Nnaji

Wani bincike da jaridar Premium Times ta yi ya nuna cewa, ministan kimiyya da fasaha da ya yi murabus din bai kammala jami'ar Najeriya (UNN) ba.

Bincike ya rahoto Simon U. Ortuanya, shugaban jami'ar UNN yana cewa, Nnaji bai kammala karatunsa ba, kuma ba a bashi wata takardar digiri ba, duk da ya shiga jami'ar a 1981.

Rahoton jaridar ya kuma ce hukumar yiwa kasa hidima (NYSC) ta tabbatar da cewa takardar NYSC da Nnaji yake amfani da ita na da alamar tambaya, kuma za ta iya zama ta bogi.

Kara karanta wannan

Uche Nnaji: Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi, ya fito ya yi bayani

Gwamnati ta yi martani game da minista

Tun da fari, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta yi martani kan zargin yin amfani da takardun bogi da ake yi wa ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin da ya dace da zarar kotu ta yanke hukunci kan zargin da ake yi wa ministan.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu, ya ce gwamnati za ta girmama tsarin shari’a kuma za ta jira hukuncin kotu kafin ta ɗauki matsaya kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com