Akpabio Ya Yi Maganar Farko bayan Bude Majalisa da Dawowar Sanata Natasha
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce Majalisa ta 10 za ta kasance mai gaskiya da amsa bukatun jama’a kai tsaye
- Ya bukaci ‘yan majalisa su mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki, ilimi, kiwon lafiya, da rage tsadar rayuwa a kasar nan
- Akpabio ya ce tarihi zai tuna da Majalisar Dattawa a matsayin ginshikin gaskiya da haske ga dimokuradiyya a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sake tabbatarwa ‘yan Najeriya ci gaban da za su kawo.
Akpabio ya ce Majalisar Dattawa ta 10 a karkashin shugabancinsa za ta kasance mai bude komai, gaskiya, da amsa bukatun jama’a kai tsaye.

Source: Facebook
Godswil Akpabio ya sake ba yan Najeriya hakuri
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a Abuja yayin zaman majalisar bayan dawowa da ta yi a yau Talata 7 ga watan Oktoban 2025, cewar rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a zaman farko bayan hutu na makonni 10, Akpabio ya ce sun san duk irin korafin da yan Najeriya game da su.
Ya ce:
“Muna jin ku ‘yan Najeriya. Ba mu da hujja, natija kuke nema, ba magana kuke so ba, aiki da canji ne kuke so.”
Akpabio ya kara da cewa Majalisar za ta bude kanta ga bincike da kulawa, saboda “lallai gaskiya da amana sune jinin dimokuradiyya.”
Ya kuma sake tabo batun yan Najeriya inda ya ce suna sane ba korafi yan kasar ke bukata ba illa aiki tukuru ba tare da wasa ba.
Shugaban majalisar ya kuma jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da wadanda ke fuskantar yunwa da tsaro.
Ya ce lokaci ya yi da ‘yan majalisa za su jajirce, su dora kan daga inda aka tsaya kan dokoki masu tasiri ga al’umma.
Ya ce:
“Ba korafi ake bukata daga gare mu ba, aiki ake jira — domin tsadar rayuwa da rashin wuta suna damun jama’a sosai.”

Kara karanta wannan
Zargin kisan Kiristoci: Kungiyar CAN ta fadi matsayarta kan rade radin a Najeriya
- Godswill Akpabio

Source: Facebook
Shawarar Godswill Akpabio ga yan majalisa
Shugaban majalisar jaddada cewa dole ne Majalisar ta hada kai da bangaren zartarwa wajen kawo gyare-gyaren tattalin arziki, ilimi da kiwon lafiya, da kuma tabbatar da dama ga matasa.
Ya kuma bukaci su karfafa tsarin mulki domin dimokuradiyya ta zama cikakkiya domin samar da ababan more rayuwa, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Akpabio ya kammala da kira ga ‘yan majalisa su tsaya tsayin daka wajen yin doka da sa ido, tare da kare mutuncin Majalisar da masu wakilci na gaskiya.
Natasha ta koma majalisa bayan dakatar da ita
Mun ba ku labarin cewa bayan dakatar da ita na wata shida, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma bakin aiki a zaman Majalisar Dattawa na yau Talata 7 ga watan Oktoban 2025.
Natasha ta isa zauren Majalisa da misalin karfe 11:52 na safe jim kadan bayan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karbi jagorancin zaman.
Rahotanni sun nuna cewa Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta gaisa da wasu sanatoci kafin ta zauna a kujerarta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

