Farfesa Mahmood Yakubu Ya Sauka daga Mukamin Shugaban INEC
- Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC bayan karewar wa'adinsa na biyu
- Yakubu ya mika ragamar shugabancin hukumar ga May Agbamuche, wacce za ta rike INEC kafin nadin sabon shugaba
- Tun a shekarar 2015, marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada Mahmood Yakubu a matsayin shugaban INEC na kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa'adinsa na shekaru 10 kamar yadda doka ta tanada.
A yau Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, Farfesa Yakubu ya mika ragamar jagorancin INEC ga May Agbamuche a matsayin mukaddashin shugabar hukumar.

Source: Facebook
Farfesa Mahmood Yakubu ya bar kujerar INEC
Channels tv ta ruwaito cewa Agbamuche ita ce babbar kwamishina mafi dadewa a aiki a hukumar zaben Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Yakubu ya sanar da haka ne a ranar Talata yayin ganawarsa da kwamishinonin zaɓe na jihohi a hedikwatar INEC da ke Abuja.
Ya bukaci kwamishinoni da daraktocin INEC su bai wa Agbamuche cikakken goyon bayan har zuwa lokacin da za a naɗa sabon shugaban hukumar.
Hakan dai na nufin Farfesa Mahmud Yakubu ya bar kujerar shugaban hukumar INEC bayan ya kammala wa’adinsa biyu na tsawon shekaru 10.
Ana sa ran Shugaba Bola Tinubu zai naɗa wanda zai gaje shi nan ba da jimawa ba, bisa amincewar majalisar dattawa.
Yadda Yakubu ya kafa tarihi a hukumar INEC
Yakubu ya zama shugaban INEC ne a watan Nuwamba 2015 lokacin da tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari ya naɗa shi, watanni shida bayan hawansa mulki.
Ya kammala wa’adinsa na farko a shekarar 2020, inda daga bisani Shugaba Buhari ya sake naɗa shi karo na biyu, in ji rahoton Daily Trust.
Hakan ya sa Farfesa Mahmood Yakkubu ya zama mutum na farko da ya shugabanci hukumar zaben Najeriya watau INEC na tsawon wa'adi biyu.
Yakubu ya gaji Farfesa Attahiru Jega, inda a zamaninsa hukumar INEC ta gudanar da manyan zaɓuɓɓuka da dama, ciki har da na 2019 da kuma 2023.
Shugaba Tinubu zai nada shugaban INEC
A halin yanzu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ke da ikon nada wanda zai gaji Farfesa Mahmood Yakubu tare da amincewar Majalisar Dattawa.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa, sun nuna cewa Shugaba Tinubu ya fara karkata kan Farfesa Joash Ojo Amupitan, SAN, dan asalin jihar Kogi a matsayin wanda zai gaji Yakubu.

Source: Twitter
Sai dai har yanzu babu wata sanarwa a hukumance, amma bayan tafiyar Farfesa Yakubu, ana sa ran kowane lokaci daga yanzu Tinubu na iya sanar da wanda ya zaba.
Jam'iyyu sun kawo mafita kan nadin shugaban INEC
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyun siyasa da ke da rajista karkashin inuwar Inter-Party Advisory Council (IPAC), sun ba da shawara kan nadin shugaban hukumar INEC.
Sun nemi a kafa sabuwar hukuma mai zaman kanta wacce za ta riƙa naɗa shugaban INEC, kwamishinoni da sakatare na hukumar zaben Najeriya.
A cewarsu, tsarin yanzu da ake amfani da shi wanda shugaban kasa ke nada shugaban INEC, ya take 'yancin da hukumar ke da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


