Wata Sabuwa: Ana Zargin Sanata da Yi Wa Wata Tsohuwa Kwacen Gida a Abuja

Wata Sabuwa: Ana Zargin Sanata da Yi Wa Wata Tsohuwa Kwacen Gida a Abuja

  • Wata tsohuwa mai shekara 84 a duniya ta zargi Osita Izunaso da yi mata karfa-karfa kan kan gidan da ta saya da kudinta
  • Matar wadda take matsayin Fasto, ta yi zargin cewa Sanatan ya kwace mata gidan da ta saya tun a shekarar 2009
  • Sai dai, Sanata Izunaso ya fito ya kare kansa daga zargin, inda ya bayyana yadda aka yi har gidan ya zo hannunsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Osita Izunaso, ya kare kansa kan zargin cewa ya yi wa wata fasto mai shekaru 84, Esther Jesulanke, kwacen gida a Abuja.

Sanata Osita Izunaso ya musanta cewa ya yi wa matar kwacen gida, inda ya ce bai yi wata mu’amalar kuɗi da ita ba.

Sanata Izunaso ya kare kansa kan zargin kwace gida a Abuja
Sanatan Imo ta Yamma, Osita Izunaso. Hoto:@EleluAyoola
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Sanata Izunaso, ya mayar da martani ne kan zargin da Esther Jesulanke ta yi.

Kara karanta wannan

Yadda wani 'dan Nijar yake yaudarar mata ya karbi kudi daga hotunan tsiraicinsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya bayyana cewa ya saya gidan ne daga wata tsohuwar alkali mai ritaya, Grace Inyang, wadda ya fara biyan N5m a matsayin kuɗin shigar ciniki.

Ya ce Grace Inyang, wadda ta rasu yanzu, ta sake sayar da gidan ga wani tsohon dan majalisa, Mohammed Jega, wanda daga baya ya sayar da shi ga Jesulanke.

Yadda zargin kwacen gidan ya fara

A wani taron manema labarai a Legas, Fasto Jesulanke ta bayyana cewa Sanata Izunaso ya tilasta mata barin gidan da ta saya N50m a shekarar 2009.

Ta ce ta saya gidan ne daga Hon. Mohammed Jega, wanda shi ne daraktan kamfanin Taulahi Investment Nig. Ltd.

Martanin da Sanata Izunaso ya yi

Sanata Izunaso ya ce wadda ya saya gidan a hannunta ne ta sake sayar da shi ga wani daban.

“Ban san ta ba. Ban ma san tana zaune a gidan ba kafin a kore ta. Wadda na saya gidan daga gare ta, Grace Inyang, ita ce ta sake sayar da shi ga Hon. Jega."

Kara karanta wannan

Uche Nnaji: Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi, ya fito ya yi bayani

"Ban ma san cewa Jega ya sayar da gidan ga Jesulanke ba sai bayan da aka kai kara gaban kotu.”
“Na biya kuɗin farko ga Grace Inyang kafin ta rasu. Saboda haka ni ba ni da wata hulɗa kai tsaye da Jesulanke. Lokacin da Hon. Jega ya gano cewa gidan ana shari’a kansa, sai ya sayar da shi ga Jesulanke.”
"Kamata yi matar nan ta tattauna da Hon. Jega, ba da ni ba. Na samu hukuncin kotu da ya tabbatar cewa gidan nawa ne, kuma ma’aikatan kotu ne suka cire kayanta daga cikin gidan, ba ni da kaina ba.”

- Sanata Osita Izunaso

Ya amince cewa bai gama biyan kuɗin gidan ba, amma ya riga ya kulla yarjejeniyar saye kafin Grace Inyang ta sayar da gidan ga Jega.

An zargi Sanata Izunaso da yin kwacen gida a Abuja
Sanata Osita Izunaso a zauren majalisa. Hoto: @EleluAyoola
Source: Twitter

Me Jega ya ce kan lamarin gidan?

Da yake magana da manema labarai, Hon. Mohammed Jega ya ce lallai ya sayar da gidan ga Jesulanke.

Sai dai, ya bayyana cewa bai san cewa ana shari'a kan gidan ba lokacin da ya saya daga wajen Grace Inyang.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bukaci diyyar N100bn bayan tsohon kwamishina ya kira shi barawo a Facebook

Sanata Natasha za ta koma majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta kammala wa'adin dakatarwar da aka yi mata.

Sanata Natasha ta shirya koma bakin aiki domin ci gaba da wakiltar mutanen mazabarta a majalisar dattawa.

Lauyoyinta sun ja kunnen majalisa kan kada a yi yunkurin hana ta komawa bakin aiki, domin hakan zai sabawa doka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng