Yadda Wani 'Dan Nijar Yake Yaudarar Mata Ya Karbi Kudi daga Hotunan Tsiraicinsu
- Wasu mata a Kano sun shiga gagarumar matsala bayan hotuna da bidiyon tsiraicinsu ya fada hannun 'dan damfara da ya ce kasuwanci ya ke yi
- Wani matashi da ke kiran kansa da Yusuf Sidi, 'dan asalin kasar Nijar da a yanzu haka yake zaune a Libya ya na yi wa matan dadin baki har ya samu hotunansu
- Rahotanni sun bayyana cewa daga bisani, yana yi masu barazana a kan ko dai su biya kudi, ko ya saki bidiyonsu da hotuna jama'a su sha kallo a duniya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wata mata mai shekaru 29 daga Najeriya ta shiga cikin tsananin damuwa bayan wani ta fada tarkon wani matashi da ke zaune a kasar Libya.
Matashin, wanda ya bayyana kansa a matsayin Yusuf Sidi, ya kan kira mata da wata lamba da ta fara daga +44 – wanda ke alamta kiran daga Birtaniya ne, tare da kulla soyayya da matan.

Source: Original
Matashi 'dan Nijar na yaudarar mata a Kano
A wani sako da fitaccen 'dan jarida, Nasiru Salisu Zango ya wallafa a Facaebok, an gano mutumin 'dan asalin Nijar kan fara yi wa matan zakin bayi har ya tura masu kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan sai ya fara neman hotuna da bidiyon tsiraici duk da sunan soyayya, idan kuwa aka yi sake sai matan su turo masa.
Amma idan an kwana biyu, sai ya kira wacce tsautsayi ya fada kanta, ya kuma shaida mata cewa shi 'dan kasuwa ne, ko ta sayi hotuna ko a zuba su duniya ta yi kallo.

Source: Facebook
Zango ya wallafa cewa:
"Da farko, ya nuna alamar kulawa da soyayya, yana fadin cewa yana yawan zuwa London don harkokin kasuwanci. A hankali ya fara aika mata da kudi, yana karfafa mata gwiwa da nuna cewa yana da niyyar yin aure da ita. Wannan tausayi da janyo hankalin ya sa matar ta yarda da shi — har ta fara aika masa da hotunanta na sirri."
"Ba da jimawa ba, sai ya bukaci a yi video call, wanda daga bisani ya nade shi. Da zarar ya mallaki hotuna da bidiyon tsirara, sai ya canza salon magana — ya fara barazanar cewa zai saka hotunan a Facebook, Instagram, da WhatsApp, har ma da neman masu siya."
Mata sun aika wa 'dan damfara kudi
Rahoton ya ci gaba da cewa a tsorace, matar ta fara aika masa da kudi don ya daina barazana gare ta, inda ta fara aika N50,000 sai ta kai kusan Naira miliyan 2.5.
A cewar matar, Yusuf ya bukaci ta sayi hotunan nata da suka kai kimanin miliyan uku idan ba haka ba zai tabbatar da ikirarin sakinsu ga duniya.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mutumi yana amfani da hanya iri daya wajen yaudarar mata da dama a Najeriya da Nijar.
Hukumar Hisbah ta Kano, ta bakin Shugabanta, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shawarci mata da su rike mutuncin da Allah SWT ya yi masu.
Ya kuma gargadi matashin da ya ji tsoron Allah SWT, domin turbar da ya ke kai ba za ta kai shi ga kyakkyawan karshe ba.
An kama matashi kan kisan kai
A baya, mun wallafa cewa bayan dogon bincike na kusan shekaru biyu, rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta samu nasarar kama wani mutum da ake zargi da garkuwa da wani basarake.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa kamun ya biyo bayan cikakken aiki na sirri da kuma hadin gwiwa tsakanin ‘yan sanda da mutanen gari da suka bayar da bayanai masu amfani.
A yayin kamun, jami’an tsaro sun bayyana cewa an yi amfani da bayanan da al’umma suka samar tare da amfani da fasahar bincike domin gano inda aka boye wanda ake zargin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


