Dangote Ya Rage Kudin Gas na Girki, ’Yan Kasuwa za Su Daidaita Farashi

Dangote Ya Rage Kudin Gas na Girki, ’Yan Kasuwa za Su Daidaita Farashi

  • Alhaji Aliko Dangote ya tabbatar da rage farashin gas din girki (LPG) a matatarsa domin saukaka wa ’yan Najeriya
  • Matakin zai taimaka wajen daidaita farashinsa a kasuwar cikin gida, musamman a lokacin karancin gas a wasu yankuna
  • Kamfanin mai na NNPCL ya yaba da wannan mataki na Dangote, yana kiran shi da ci gaba mai kyau ga tattalin arzikin kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Rahotanni na nuni da cewa matatar Dangote ta sanar da rage farashin gas din girki (LPG).

Saukin farashi ya zo ne da nufin tallafawa tattalin arzikin cikin gida da kuma tabbatar da wadatar gas a kasuwa.

Wajen sayar da gas da hoton Dangote
Wajen sayar da gas da hoton Dangote. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wani rahoto da Nairametrics ta wallafa a X ya nuna cewa an samu saukin ne a lokacin da aka shiga karancin gas a Najeriya.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: An nemi Ministan Tinubu ya yi murabus, ya mika kansa ga hukuma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon farashin gas din Dangote

Rahoton da Legit ta wallafa ya nuna cewa Dangote ya sauke farashin daga N810 zuwa N760 a kan kowane kilo.

Dangote ya zama wanda ke da mafi karancin farashin gas a kasuwar cikin gida a Najeriya bisa yadda rahotanni suka nuna.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu kamfanoni masu zaman kansu irin su Matrix da Ardova ke sayar da gas a N920.

A.Y.M Shafa da NIPCO kuma suna sun tsayar da shi a kan farashin N910, sai kuma Stockgap da ya fi tsada a kan N950.

Wannan na nufin akwai bambancin kudi daga N150 zuwa N190 tsakanin Dangote da sauran kamfanoni.

Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote
Attajirin Afrika, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

NNPCL ta yaba da matakin Dangote

Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya jinjinawa Dangote bisa sauke farashin, yana mai cewa matakin zai taimaka wajen daidaita kasuwa da tabbatar da wadatar kayayyaki.

Jami’an NNPCL sun bayyana cewa za a dauki wasu kwanaki kafin tasirin rage farashin ya bayyana a ko ina.

Kara karanta wannan

PENGASSAN ta hukunta rassanta 2 kan rashin hana Dangote gas a yajin aiki

Kamfanin ya kuma bayyana cewa zai hada kai da Dangote wajen tabbatar da wadatar iskar gas a kasuwa da kuma dakile tsadar shi.

Matsalar karancin gas a Najeriya

Mutanen Legas da wasu jihohin Kudu maso Yamma sun shafe kwanaki suna fama da karancin gas na girki.

Shugaban kungiyar masu sayar da gas na Najeriya (NALPGAM), Olatunbosun Oladapo, ya tabbatar da cewa wannan karanci bai shafi kasa baki daya ba, sai dai Kudu maso Yamma.

Olatunbosun Oladapo ya ce Kudu maso Kudu da Gabas suna da isasshen gas, sai dai Kudu maso Yamma ta fuskanci karanci saboda tsaiko da aka samu.

Ya bayyana cewa bayan gyara da aka yi a matatar Dangote, kungiyar ma’aikata ta PENGASSAN ta fara yajin aiki wanda ya jinkirta jigilar gas.

Yanzu da aka dawo da aikin gadan gadan, ya ce ana sa ran share cunkoson cikin kwanaki biyu zuwa uku.

An yi zanga-zanga kan Dangote

A wani rahoton, kun ji cewa masu matasa sun yi zanga zangar nuna goyon baya ga matatar Dangote a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Abba ta shirya kashe N1.6bn don auren gata a jihar Kano

Masu zanga zangar sun bayyana cewa suna adawa da duk wani mataki da zai iya kawo cikas da matatar.

Baya ga haka, sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya hana shigo da mai da aka tace daga ketare.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng