Majalisa: Za a Buga Muhawara kan Zargin Yi wa Kiristoci Kisan Kiyashi a Najeriya

Majalisa: Za a Buga Muhawara kan Zargin Yi wa Kiristoci Kisan Kiyashi a Najeriya

  • A ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025 ne majalisun kasar nan za su dawo domin ci gaba da aikin samar da dokokin da za su kawo ci gaban kasa
  • Daga batutuwan da za a saka a gaba shi ne yadda wasu tsirarun mutane a kasashen waje, musamman Amurka ke cewa an taso kiristocin Najeriya a gaba
  • Sanata Ali Ndume da wasu Sanatoci sun dauki nauyin kudurin da zai sun dauki nauyin kudurin kare sunan kasar a idon duniya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Dattijawan kasar nan za ta fara zaman dawo hutu a yau da wani kuduri na gaggawa da ke neman kore labaran da ke cewa ana kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Abba ta shirya kashe N1.6bn don auren gata a jihar Kano

A baya-bayan nan wasu kafafen kasashen waje da kungiyoyi suka rika yada cewa an tas kiristoci a gaba, ana yi masu kisan gilla ba dare ba dare.

Za a yi magana kan zargin ware kiristoci ana kashe su a Najeriya
Hoton zauren majalisar dattawa da Sanataci Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan ta sa Sanata Mohammed Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu ya dauki nauyin kudiri domin muhawara a kan batun a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa: Sanatocin da su ka goyi bayan Ndume

Arise News ta ruwaito Sanata Sani Musa (Niger ta Gabas), Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko (Sakkwato ta Arewa), da Sanata Ibrahim Bomai (Yobe ta Kudu) ne za su taya Ndume gabatar da kudirin.

Rahotanni sun bayyana cewa kudirin na da nufin mayar da martani ga majalisar dokokin Amurka, wacce ta ayyana Najeriya a matsayin kasar mai hatsarin saboda gallaza wa Kiristoci.

Sun yi wa kudurin, mai taken: “Bukatar gaggawa don gyara mummunar fahimta game da labarin kisan kiristoci a Najeriya.”

Sanatocin na ganin cewa irin wannan labari na iya rura wutar wariyar addini, bata sunan Najeriya a idon duniya, da kuma durkusar da hadin kan kasa.

Ndume: "Kowa ya ji illar rashin tsaro"

Kara karanta wannan

Ana barazanar shigar da gwamnoni 36 da Wike kotu kan kudin tallafin mai

A cikin bayanan da ke cikin kudurin, Sanata Ndume ya bayyana cewa, ko da yake Kiristoci sun fuskanci hare-hare a wasu sassa, Musulmai da sauran kabilu sun fuskanci irin wannan.

Majalisar za ta nemi gwamnatin tarayya da ta fitar da bayanan da suka shafi gaskiya da adadi, tare da bayar da hujjojin adadin mutanen da aka kashe domin yin gyara ga labarin karya.

Ndume ya ce da Musulmi da kirista, kowa na jin jiki a Najeriya
Hoton tsohon mai tsawatarwa a majalisa, Ali Ndume Hoto: Sen Muhammad Ali Ndume
Source: Facebook

Za a kuma nemi ofishin harkokin wajen Najeriya da hukumomin tsaro da su hada gwiwa wajen tsara sabuwar hanyar sadarwa da za ta fayyacae gaskiya kan hari a kasar nan.

Haka kuma Sanatocin za su bukaci manyan kafofin yada labarai na waje da ofisoshin jakadanci, musamman na Amurka, da su nemi sahihan labarai daga Najeriya.

Kudurin zai kuma bukaci hukumomin Najeriya su tabbatar da adalci ga dukannin wadanda suka rasa rayukansu ko dukiyarsu, ko Kiristoci ne, Musulmai ko kuma wasu daban.

An yi magana kan kisan kirstoci a Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Reno Omokri, tsohon mataimakin mashawarci ga shugaban kasa, ya kalubalanci rahoton da wani gidan rediyo na Amurka na cewa ana gallaza wa kiristocin kasar nan.

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

Gidan rediyon ya rika yada cewa Najeriya ,ana kashe Kiristoci sama da 500,000 a wani abu mai kama da an saka su a gaba saboda addininsu, lamarin da ya fara daukar hankalin Amurkawa.

Omokri ya ce ikirarin cewa an kashe Kiristoci ne yana cikin labaran ƙarya da farfaganda, domin rura wutar ƙiyayya tsakanin addinai da jawo rashin zaman lafiya a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng