Yadda Gwamnatin Abba Ta Shirya Kashe N1.6bn don Auren Gata a Jihar Kano
- Gwamnatin Kano ta fara shirin daurar da marayu da marasa aure a cikin tsarinta na auren gata da aka saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci a jihar
- A wannan karo na biyu da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ke daukar nauyin auren, ta amince da Naira biliyan 1.6 domin tabbatar da komai ya tafi sumul
- Daga cikin kudin, za a biya kudin lefe, kayan dakunan amarya da shirya bikin aure karkashin kulawar Ma'aikatar Harkokin Addini ta jihar
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 1.6 domin aiwatar da zagaye na biyu na shirin aurar da marayu da marasa aure a fadin jihar.
Kwamishinan yada labarai, Ibrahim A Waiya ya ce wannan na daga cikin shirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na tabbatar da walwalar jama'a.

Source: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da ya kunshi ayyuka da kudin da aka ware masu bayan zaman majalisa, Waiya ya ce an ware N1.6bn ga ma'aikatar addinai don auren.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya amince da wannan kudi ne domin tallafa wa mazan da suka rasa matansu da matan da suka rasa mazansu don ba su damar sake gina rayuwar aure mai cike annashuwa.
Gwamnati za ta yi auren gata a Kano
21st century chronicle ta ruwaito cewa bayan taron majalisar zartarwa karo na 32 a Kano, Kwamred Wayya ya yi karin bayani a kan zaman da gwamna Abba ya jagoranta.
Kwamishinan ya bayyana cewa wannan shiri zai hada da samar da dakunan amarya, biyan kudin lefe, da kuma shirya bukukuwan aure ga ma’auratan da suka cancanta .
Ya kara da cewa za a gudanar da shagalin bikin a karkashin kulawar Ma’aikatar Harkokin Addini ta jihar Kano kamar yadda aka saba.

Kara karanta wannan
Hadimin gwamna ya fusata, ya ajiye mukami bayan sauya shekar Eno zuwa APC a Akwa Ibom
Dalilin gwamnatin Kano na yin auren gata
Kwamred Wayya ya ce shirin na da nufin rage yawan zawarawa da marasa aure a cikin al’umma, da karfafa dangantaka tsakanin iyalai.
Haka kuma ana sa ran zai tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin mazauna jihar tare da dawo da martabar aure kamar yadda ya ke a baya.

Source: Facebook
Kwamishinan ya shawarci wadanda za su amfana da wannan dama da su kasance masu gaskiya da rikon amana.
Kwamred Ibrahim Wayya ya kuma umarce su da su yi amfani da wannan dama wajen gina auren da zai dore cikin nasara da zaman lafiya.
Gwamnatin Kano ta waiwayi tubabbun 'yan daba
A baya, mun wallafa cewa Hukumar Hisbah ta jihar ta sanar da cewa za ta dauki nauyin aurar da matasa da suka tuba daga ayyukan daba domin kara inganta rayuwarsu, su zama na gari.
Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya sanar da haka yayin da yake jawabi ga wasu matasa da suka zubar da makamai da abin da ya shafi tashin hankali a jihar.
Sheikh Daurawa ya ce wannan shiri wani bangare ne na manufofin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin matasa sun samu rayuwa mai inganci, da kuma inganta zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

