Kwana Ya Kare: Tsohon Babban Sojan Najeriya Ya Rasu a Cikin Jirgin Saman Abuja
- Jirgin saman British Airways ya yi saukar gaggawa a Barcelona da ke Spain bayan mutuwar daya daga cikin fasinjojinsa
- Wani tsohon jami'in rundunar sojin saman Najeriya ne ya mutu a hanyar dawowa gida domin neman magani
- Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya taso ne daga birnin Landan na kasar Birtaniya da nufin zuwa Abuja a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon jami'in rundunar sojin saman Najeriya wanda ya kai matsayin Air Vice Marshal ya rasu a cikin jirgin sama bayan tasowa daga Landan zuwa Abuja.
Tsohon babban sojan ya mutu ne a cikin jirgin kamfanin British Airways, lamarin da ya tilasta wa jirgin sauka a Barcelona da ke kasar Spain da safiyar yau Litinin.

Source: Getty Images
Jaridar Daily Trust tattaro cewa jirgin ya tasondaga filin jirgin sama na Heathrow, da ke London, da karfe 11:00 na dare ranar Lahadi, 5 ga Oktoba, 2025 da nufin zuwa Abuja, Najeriya.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu zai fito bainar jama'a kan zargin amfani da digirin bogi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya faru a jirgin British Airways
A bisa yadda aka tsara tafiyar, jirgin zai sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe, Abuja, da karfe 5:00 na safiyar yau Litinin.
Sai dai da misalin karfe 1:30 na dare, matukin jirgin ya sanar da fasinjoji cewa an samu matsalar rashin lafiya, sannan ya yi kwana zuwa filin jirgin sama na El Prat, Barcelona.
Majiyoyi sun shaida cewa mamacin, wanda ake kyautata zaton ya kai shekara 80, ya dade yana fama da rashin lafiya, kuma an dauko shi zuwa Najeriya ne domin ci gaba magani, lokacin da ya rasu a tsakiyar tafiya.
Marigayin yana daya daga cikin ’yan tsirarun tsofaffin Air Vice Marshal daga jihar Anambra a Kudancin Najeriya.
Halin da mutane suka shiga a jirgin sama
Rasuwar tsohon sojan ta tayar da hankalin fasinjoji, inda aka ruwaito cewa wata mata mai juna biyu ta shiga wani hali sakamakon abin da ya faru.

Kara karanta wannan
Bayan soke fareti, Tinubu ya fadi abin da ya faru da shi a daren 1 ga Oktoba 2025
Kamfanin British Airways, a wata sanarwa, ya aike da sakon neman afuwa ga fasinjoji kan tsaikon da aka samu, tare da tabbatar musu da cewa yana tare da su.
Sanarwar ta ce:
“Fasinjoji su saurari sakon da za mu turo masu domin karin bayani, ko su tuntube mu ta hanyar Live Chat don neman taimako.
"Kamfanin British Airways ya fahimci cewa hakan ya jawo musu cikas, kuma ya gode bisa hakurin da suka yi."

Source: Getty Images
An sauya jirgin da zai kawo fasinjojin Abuja
Kamfanin ya kuma tabbatar da cewa ya turo wani jirgin saman da zai kwashi fasinjojin zuwa Abuja.
Da farko an tsara jirgin zai tashi daga Barcelona da karfe 2:00 na rana agogon kasar Spain, ya isa Abuja da 7:00 na yamma.
Sai dai daga baya an sake sauya lokacin tashin jirgin zuwa 2:50 na rana, tare da isa Abuja da misalin 5:45 na yamma agogon Najeriya, in ji rahoton Leadership.
Jirgin Ibom Air ya yi saukar gaggawa a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa jirgin saman Ibom Air ya yi gaggawar komawa filin jirgin saman Abuja sakamakon rashin lafiyar wata mata.

Kara karanta wannan
Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa
An tattaro cewa jirgin ya tashi daga Abuja da nufin zuwa Legas, amma ya yi kwa ya dawo saboda matsanancin halin da wata fasinja ta shiga.
Wannan al'amari ya jawo tsaiko ga jirgin saman, wanda daga baya ya sake tashi zuwa jihar Legas kamar yadda aka tsara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng