Gwamna AbdulRahman Ya Ciri Tuta, Ya ba Ma'aikata Hutun Kwana 1 a Jihar Kwara
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ba ware Litinin, 6 ga Oktoba, 2025 a matsayin ranar hutun kwana daya ga malamai a jihar Kwara
- Kwamishinan ilimi, Dr. Lawal Olohungbebe, ya ce Gwamna AbdulRahman ya amince da hutun ne don murnar Ranar Malamai ta Duniya
- Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da UNESCO da UNICEF suka ce ana bukatar karin malamai miliyan 44 a duniya kafin 2030
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ayyana Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, a matsayin ranar hutu na musamman a jihar.
Gwamna AbdulRahman ya ba da hutun kwana dayan ne ga malaman makaranta domin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta shekarar 2025.

Source: Twitter
An ba malamai hutu a Kwara
Gidan rediyon Sobi FM da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara ne ya rahoto sanarwar ba da hutun a labarin da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta fito ne daga kwamishinan ilimi da ci gaban dan adam na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, wadda aka rabawa manema labarai a Ilorin.
A cikin sanarwar, Gwamna AbdulRahman ya yabawa malamai bisa juriya, sadaukarwa da kishin aiki, yana mai cewa su ne ginshikin ci gaban dan Adam da cigaban kasa.
“Malamai suna taka muhimmiyar rawa wajen gina al’umma, su ne ke tsara tunani da dabi’un matasa domin gina nagartacciyar kasa."
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq.
Kwamishinan ya kara da cewa malamai suna zama abin koyi ta fuskar dabi’un hakuri, jajircewa da ƙoƙari — manyan dabi’u da ake bukata wajen gina shugabannin gaba.
'Ana bukatar karin malamai miliyan 44 a duniya'
A yayin da Najeriya ta shiga sahun sauran kasashe wajen bikin Ranar Malamai ta Duniya, UNESCO, UNICEF, ILO da Education International sun yi tsokaci mai muhimmanci.
Kungiyoyin sun bayyana cewa duniya na bukatar karin malamai miliyan 44 domin cimma manufar ilimin firamare da sakandare ga kowa kafin shekarar 2030, inji rahoton ThisDay.

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
A cikin sakon hadin gwiwa da suka fitar don bikin ranar na bana, kungiyoyin sun bukaci gwamnatoci da abokan hulda su tabbatar da cewa hadin kai ya zama ginshiki a harkar koyarwa.
Kungiyar ASUSS ta nuna takaici kan yadda wasu gwamnatoci ba su aiwatar da tsarin daidaita shekarun ritaya na malamai ba, tana cewa hakan na rage musu kwarin gwiwa.

Source: UGC
Ranar Malamai ta Duniya da taken bana
Ranar Malamai ta Duniya ana gudanar da ita ne duk shekara a ranar 5 ga Oktoba domin girmama malamai a fadin duniya.
Ana tunawa da ranar da aka amince da shawarwarin ILO/UNESCO na 1966 da suka kafa dokoki kan ‘yancin malamai, horo, daukar aiki da yanayin koyarwa.
Taken bikin bana shi ne, “Inganta harkar koyarwa a matsayin aikin da ya shafi kowa”, kuma ya jaddada muhimmancin hadin kai, jagoranci da tallafawa juna tsakanin malamai da shugabannin makarantu.
An karo darussa a makarantun sakandare
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnati ta gabatar da sababbin darussan karatu a makarantun sakandare da za su fara aiki daga 2026.
Sabon tsarin karatun da aka kawo ya mayar da hankali ne kan koyar da dalibai fasahar zamani da kasuwanci tun daga matakin karamar sakandare (JSS).

Kara karanta wannan
Gwamna ya bukaci diyyar N100bn bayan tsohon kwamishina ya kira shi barawo a Facebook
Darussan da za a rika koyarwa yanzu sun haɗa da Cybersecurity, Python, JavaScript, AI, da kuma koyon yarukan duniya irinsu Sinanci da sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
