Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki

Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki

- Shugaba Muhammadu Buhari ya yarda da biyan albashi na musamman ga malaman makaranta

- Har ila yau shugaban kasar ya kara wa malaman shekarun aiki daga 35 zuwa 40

- Adamu Adamu, ministan ilimi ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da biyan albashi na musamman ga malamai.

Shugaban kasar ya kuma kara wa’adin shekarun aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40, jaridar This Day ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai

Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki
Yanzu yanzu: Buhari ya amince a ƙarawa malamai albashi da shekarun aiki Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba.

Ya bayar da sanarwar ne a cikin wani jawabi na musamman da ya karanto yayinda yake wakiltan shugaban kasar a wajen taron zagayowar ranar malamai ta duniya.

Zuwa yanzu dai ba a san yadda tsarin zai kasance ba.

KU KARANTA KUMA: Sabbin zafafan hotunan Nafisa Abdullahi kusa da dankareriyar motarta

A wani labarin kuma, Sunday Dare, ministan matasa da bunkasa wasanni, ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin daukar matasa miliyan daya aiki.

Dare ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar makon da ya gabata, a yayin wani bukin baje kolin kasuwanci na fasahar matasa a babban birnin tarayya Abuja.

Ma'aikatar matasa da bunkasa wasanni tare da hadin guiwar gidauniyar 'I Choose Life' (na zabi rayuwa) suka shirya taron.

An shirya taron ne domin bukin murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun 'yanci, da kuma taya matasa murna kan nasarar da suka samu a kasuwanci, kirkira, aikin hannu da fasahar zamani.

Taken taron shi ne, 'Mafarkin kasata Nigeria,' kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar Dare, ma'aikata matasa da bunkasa wasanni na hada karfi da karfe da sauran ma'aikatu don samar da ayyukan yi, lamarin da zai tabbata kafin karshen watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel