Gwamna Ya Lallaba Ya Gana da Tinubu, Za a Saki Jagoran 'Yan Ta'adda da Buhari Ya Kama a 2021
- Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
- Alex Otti ya ce tattaunawa ta yi nisa kuma nan ba da jimawa ba Tinubu zai saki shugaban kungiyar ta'adanci, IPOB, Nnamdi Kanu
- Ministan Ayyuka, David Umahi ya yi kira ga mutanen Kudu maso Gabas da su kwantar da hankulansu kuma su bi doka da oda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya ce nan ba da jimawa ba za a saki Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB da ake tsare da shi a Najeriya.
Kungiyar IPOB wacce ke fafutukar ballewa daga Najeriya na daga cikin kungiyoyin da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin na ta'addanci.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu zai saki Nnamdi Kanu?
Gwamna Otti ya sanar da shirin sako Kanu a ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu, The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ina tabbatar muku cewa muna kan tattaunawa da Shugaban Ƙasa kuma ya nuna kyakkyawar niyya a kai, tabbas nan ba da daɗewa ba Nnamdi Kanu zai samu ’yancinsa.”
“Ni da Tinubu mun dade tare a matsayin abokai tsawon shekaru. Na san idan zai yi abu zai fada maka, idan kuma ba zai yi ba, zai faɗa maka kai tsaye. Tunda ya yi alkawari, na tabbata zai cika shi.”
- In ji Gwamna Alex Otti.
Tinubu ya bukaci zaman lafiya a Kudu maso Gabas
Shugaba Tinubu, wanda Ministan Ayyuka, David Umahi, ya wakilta, ya yi kira ga al’ummar Kudu maso Gabas da su zauna lafiya tare da bin doka sau da kafa.
A rahoton Leadership, Umahi ya ce:
“Ina kira ga mutanen Kudu maso Gabas da su haɗa kai. A matsayina na ɗan uwanku, na saurari saƙonnin da aka miƙa wa shugaban kasa da kuma jawabin gwamnan Abia.”

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
“Ina tabbatar wa Sanata Abaribe da Gwamna Otti cewa gwamnonin Kudu maso Gabas na aiki tukuru, su na kokarin lalubo mafitar siyasa tare da sanatoci, ’yan majalisar wakilai da ministoci."
Yadda Tinubu ya dauki Kudu maso Gabas
Umahi, tsohon gwamnan jihar Ebonyi ya bayyana Shugaba Tinubu na son mutanen Kudu maso Gabas kuma yana su samu zaman lafiya.
Ministan ya ce:
"Ina da tabbacin cewa da soyayyar da Shugaban Ƙasa wa yankinmu, za a samu mafitar zaman lafiya.
"Amma dole mu ci gaba da bin doka, mu nuna godiya, kuma mu gane cewa wannan shugaban kasa ya sanya Kudu maso Gabas a tsakiyar harkokin ƙasa.”

Source: Facebook
Tun daga watan Yuni 2021 lokacin mulkin marigayi Muhammadu Buhari ake tsare da shugaban IPOB a hannun hukumar DSS bayan an kawo shi daga ƙasar Kenya.
Gwamna Otti ya ba sojojin Najeriya shawara
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Alex Otti ya buƙaci sojojin da su maida hankali sosai wajen tattara bayanan sirri domin daƙile matsalolin rashin tsaro tun kafin su afku.
Gwamnan ya tunatar da su cewa idan za a yi amfani da bayanan sirri yadda ya dace, to hukumomin tsaro a Najeriya za su iya daƙile aikata miyagun laififfuka.
Ya yabi sojojin Najeriya da cewa suna da horo da ladabi, inda ya bayar da misali da yadda sojojin da ke Abia suka yi aiki tare da gwamnatinsa wajen dawo da zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

