Sharudan da Trump, Netanyahu Suka Gindaya domin Tabbatar da Zaman Lafiya a Gaza

Sharudan da Trump, Netanyahu Suka Gindaya domin Tabbatar da Zaman Lafiya a Gaza

  • Shugaba Donald Trump ya bayyana shirin zaman lafiya mai matakai 20 a Fadar White House tare da Benjamin Netanyahu
  • Shirin ya tanadi sake gina Gaza, sakin fursunoni da mayar da zaman lafiya ta hanyar amincewa tsakanin ɓangarorin biyu
  • Sabon tsarin mulki na wucin gadi zai gudana a Gaza, ƙarƙashin kulawar kwamitin zaman lafiya da Trump zai jagoranta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana shirin zaman lafiya mai matakai 20 domin kawo ƙarshen yaƙi a Gaza.

Trump ya gabatar da shirin ne a Fadar White House tare da Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu domin tsagaita wuta a Gaza.

Netanyahu, Trump sun sanya sharuda kan zaman lafiya a Gaza
Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu. Hoto: Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: UGC

Gaza: Trump, Netanyahu sun gindaya sharuda

Rahoton Al Jazeera ya ce an yi hakan ne da manufar samar da zaman lafiya na dindindin da tabbatar da tsaron makwabtaka.

Kara karanta wannan

Trump ya umarci Netanyahu ya gaggauta daina luguden wuta a Gaza

A cewar shirin, za a mayar da Gaza yankin da babu ƙungiyoyin ta’addanci, sannan a fara sake gina gine-gine, asibitoci, makarantu da hanyoyi domin inganta rayuwar al’umma.

Shirin ya tanadi cewa, idan Isra’ila da Hamas suka amince, za a dakatar da yaƙi nan take, a saki fursunoni, sannan a fara shigar da tallafin jin kai da kayan gina kasa.

An kuma tsara kafa hukumar mulki ta wucin gadi wacce za ta ƙunshi ƙwararrun ‘yan Falasɗinu da masana ƙasashen waje ƙarƙashin kulawar kwamitin zaman lafiya da Donald Trump zai jagoranta.

Wannan kwamiti zai kula da gudanar da ayyukan yau da kullum da tsare-tsaren sake gina Gaza har sai Gwamnatin Falasɗinu ta kammala shirin gyaranta ta karɓi iko da kanta.

Trump ya kawo tsare-tsaren domin sake gina Gaza
Shugaban Amurka, Donald Trump yayin kamfen zabe. Hoto: Donald J Trump.
Source: Twitter

Tsare-tsaren Donald Trump na sake gina Gaza

Trump ya bayyana cewa, za a kafa yanki na musamman domin jawo zuba jari da samar da ayyukan yi, tare da tabbatar da cewa ba za a sake gina kayan yaƙi a yankin ba.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta fadi irin zaben da shugaba Tinubu ya ke so a 2027

Shirin ya kuma tanadi shirin amincewa tsakanin addinai domin sauya tunanin jama’a da tabbatar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinu da Isra’ila, kamar yadda BBC ta tabbatar.

A ƙarshe, gwamnatin Amurka za ta shirya tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu domin ƙirƙirar sabuwar hanya ta samar da ‘yancin kai da ci gaban Falasɗinu cikin lumana.

Har ila yau, idan Hamas ba ta amince da tsarin ba ko kuma ta bata lokaci, shirin ba da agaji zai ci gaba musamman a wuraren da ba su da matsalolin ta'addanci a Gaza.

Isra'ila ta farmaki masu kai agaji Gaza

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta kashe mutane 73 a Gaza tare da cafke masu fafutukar Flotilla da ke shirin kai agaji.

Sanata Chris Andrews na kasar Ireland na daga cikin waɗanda aka tsare, Sinn Fein ta ce an kama shi ba bisa ƙa’ida ba.

Hare-haren sun jawo zanga-zanga a kasashen Turai, yayin da wasu ƙasashe suka kira matakin na Isra’ila babban laifi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.