Fasto Ya Taba Musulunci a gaban Sarkin Musulmi, Ya Tashi Ya Ba Shi Amsa Nan Take a Abuja
- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya soki kalaman Bishof Kukah kan zargin Musulunci da shirin karbe mulki
- Ya ce mutane na yi wa kalmar 'Islamism' gurguwar fassara, inda ya jaddada cewa burin musulunci da musulmai a samu nagartaccen shugabanci
- Sarkin ya bayyana cewa musulmai suna da tsarin rayuwa bisa koyarwar Alkur'ani, Hadisin Manzon Allah SAW da fahimtar magabata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya karyata zargin cewa addinin Musulunci yana neman karɓe mulki a Najeriya.
Sultan na Sakkwato ya karyata wannan rade-radi, yana mai jaddada cewa burin Musulunci da musulmi shi ne samar da nagartaccen shugabanci a kasar nan.

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ce Sarkin Musulmi ya fadi haka ne a taron kaddamar da littafin “Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum” wanda tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya rubuta.

Kara karanta wannan
Babu boye boye, an ji dalilin da ya sa Bola Tinubu bai jawo matarsa ta karbi musulunci ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Musulmi ya ba Bishof Kukah amsa
A taron, wanda ya gudana a Abuja, Sarkin Musulmi ya ce:
"Bari na fara da gyara jawabin Bishof Kuka game da batun Musulunci, ina ganin ya yi kuskuren amfani da kalmar ta yadda wasu za su iya fahimtar da ba daidai ba game da Musulunci.
"Tsarin musulunci ba ya nufin karbe mulki, musulunci na son a samu kyakkyawan shugabanci a cikin al'umma."
'Musulmai sun goyi bayan Jonathan'
Sarkin Musulmin ya tuna yadda tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya samu cikakken goyon bayan Musulmi a lokacin mulkinsa.
A rahoton Ripples Nigeria, Sultan ya kara da cewa:
“Lokacin da Jonathan yake shugaban ƙasa, mun ba shi goyon baya 100 bisa 100. A tsawon lokacin mulkinsa, babu wanda ya faɗi wani abu mara kyau a kansa; shi kansa ya san haka."
"Don haka Musulunci ba kamar yadda wasu ke zato ba ne; kuskuren fahimta ne ake ɗauka kamar yana nufin yunkurin kwace mulki. Ba haka ba ne, abin da muke nema shi ne ingantaccen mulki.”
Abubuwa 3 da ke tsara rayuwar Musulmi
Ya bayyana cewa Musulmai suna da tsari da tafarkin da suke bi watau Alƙur’ani, Hadisan Annabi (SAW), da kuma magabata na kwarai, yana mai cewa Musulunci ba shi da alaka da tsattsauran ra'ayi.
"Komai rubuce yake. Muna da tsarin rayuwa, muna da Alƙur’ani Mai Girma, Hadisan Annabi (SAW), da fahimtar magabata. Waɗannan ne abubuwa uku da ke jagorantar mu.
"Duk wanda ya bar wadannan abubuwa ya faɗi abin da bai sani ba, ba daga Musulunci ba ne, saboda Musulunci bai yarda da tsattsauran ra’ayi ba.
"Ba za ka zama mai tsattsauran ra’ayi ba sannan ka ce kai Musulmi nagari ne. Don haka mu yi karatu mu fahimci waɗannan abubuwa."
- In ji Sarkin Musulmi.

Source: Facebook
Mutane sun yaba da abin da Sarkin Musulmi ya yi na fayyace rudanin tun a wurin taron, inda wasu ke cewa haka ake son jagora.
Wani dan Katsina, Abdullahi Muhammad ya shaidawa Legit Hausa cewa abin da Sarkin Musulmi ya yi shi ne daidai domin idan ana kyale irin wannan, ba a san abin da zai biyo baya.
"Galibin kiristoci suna da irin wannan tunanin, ga ni suke yi duk wani musulmi yana da tsattsauran ra'ayi, kuma ba haka yake ba, ba haka musulunci ya koyar ba.
"Sultan ya burge mutane da dama, ya ba da amsa gamsasshiya a wurin taron, Allah Ya saka masa da alheri, Ya ci gaba da jagorantar al'amuransa," in ji shi.
Sultan ya yi wa Tinubu, gwamnoni nasiha
A wani rahoton, kun ji cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya kara jan hankalin shugabanni kan sauraron koken talakawan Najeriya.
Sarkin Musulmi ya bukaci, Tinubu, gwamnoni 36 da sauran wadanda Allah ya ba shigabanci au rika sauraron bukatun jama'arsu domin akwai ranar hisabi.
Haka kuma ya bukaci yan Najeriya su kaucewa zagin shugabanni, maimakon haka su rika masu addu'ar shiriya domin su gyara ayyukansu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
