Tinubu zai Je COCIN Tattaunawa da Shugabannin Kiristocin Arewa a Filato
- Gwamnatin Filato ta sanar da rufe hanyoyi a Jos da Bukuru domin saukaka ziyarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Tinubu zai halarci jana’izar mahaifiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwada a jihar
- Bayan jana’izar, an sanar da cewa shugaban zai gana da manyan shugabannin Kiristoci daga Arewacin Najeriya a Jos
FCT, Abuja – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai kai ziyara Jihar Filato a ranar Asabar, 4, Oktoba, 2025, domin halartar jana’izar mahaifiyar shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwada.
Gwamnatin jihar ta riga ta sanar da rufe wasu manyan hanyoyi a Jos da Bukuru domin tabbatar da tsaro da saukaka zirga-zirgar motocin shugaban kasar.

Source: Facebook
Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ne ya wallafa sanarwa kan ziyarar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Kwamishinar yada labaran jihar, Joyce Ramnap ta bayyana cewa daga karfe 7:00 na safe za a rufe wasu hanyoyi da muhimman tituna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hanyoyin da za a rufe saboda zuwan Tinubu
Punch ta wallafa cewa sanarwar gwamnatin jihar ta bayyana cewa wasu tituna za su kasance a rufe tun daga safe.
Cikin su akwai hanyar Mararaban Jama’a zuwa Bukuru, Dadin-Kowa da tsohuwar hanyar filin jirgin sama zuwa Plateau Hospital, da Hillstation zuwa hedikwatar COCIN/Bankin CBN.
Kwamishinar ta yi kira ga direbobi da fasinjoji da su yi hakuri da wannan sauyi na wucin gadi, tana mai cewa an dauki matakin ne don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Jana’izar da Tinubu zai je a Filato
Shugaban kasa zai kasance a Jos domin halartar jana’izar marigayiya Nana Lydia Yilwada, uwa ga Farfesa Nentawe Yilwada, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Wannan lamari ya ja hankalin shugabannin siyasa da na al’umma daga sassa daban-daban na kasar.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa wannan ziyara ta Shugaba Tinubu alama ce ta girmamawa ga iyalin marigayiya da kuma jama’ar Filato baki daya.

Source: Twitter
Ya kara da cewa yana fatan wannan damar za ta kara hada kan jama’a da kuma gina zaman lafiya a jihar.
Caleb Mutfwang ya bukaci al’ummar Filato da su tarbi shugaban kasar, yana mai cewa wannan ziyara na iya kara fahimtar da shugaban kasa bukatun mutanen jihar.
Tinubu zai gana da shugabannin Kiristoci
Bayan kammala jana’izar, Shugaba Tinubu zai gudanar da ganawa da shugabannin Kiristoci daga Arewacin Najeriya a hedikwatar COCIN da ke Jos.
An ce ganawar na da muhimmanci wajen karfafa tattaunawa da shugabannin addini domin tabbatar da hadin kai da jituwa a tsakanin al’ummar kasar.
Fadar shugaban kasa ta ce ganawar za ta zama wata dama ta musamman ga Tinubu wajen jin ra’ayoyin shugabannin addini da kuma bayyana manufar gwamnatinsa kan ci gaban Najeriya.
Zaben da Tinubu ke son yi a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi magana kan shirin zaben 2027.
Tajudeen Abbas ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kudiri aniyar yin sahihin zabe domin tabbatar da adalci.
Shugaban majalisar ya yi magana ne yayin wata ganawa da tawagar tarayyar Turai da suka zo Najeriya kan zaben kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


