Fusatattun Matasa Sun Yi wa Matar Sarki Tsirara, an Lakadawa Sarki da Yarima Duka
- Fusatattun matasa sun kusa yi wa matar sarki tsirara yayin da suka farmaki fadar mai martaba sarkin Ose da ke jihar Ondo
- An rahoto cewa matasan sun lakadawa matar sarkin dukan tsiya bayan sun daki sarkin, sannan suka yi wa yarima jina-jina
- Sarki Moses Bakare ya nuna takaici kan wannan harin da aka kai masa da iyalansa, yayin da aka ce matasan garin ba sa son sa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Wasu fusatattun matasa, da har yanzu ba a gano ko su wanene ba, sun lakadawa sarkin Ose, Oba Moses Bakare dukan tsiya.
Matasan ba su tsaya a nan ba, an ce sun yi wa matar sarkin duka, kuma suka fara yi mata tsirara, tare da yiwa yarima Victor jina-jina.

Source: Twitter
Matasa sun lakadawa iyalin sarki duka
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Juma'a a karamar hukumar Ose da ke jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar ta ce matasan sun yi amfani da bikin doya da ake yi shekara-shekara wajen tumurmusa sarkin, da iyalansa.
An ce yayin da matasan ke dukan matar sarkin, sun cire wasu sassa na kayan jikinta, da ya sa har aka fara ganin tsiracinta.
Duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin faruwar lamarin ba, amma dai wani mazaunin garin ya ce dama matasa suna kullace da sarkin.
Matasa ba su son sarkin da aka nada masu
Mazaunin garin ya ce yanzu yana fargabar cewa za a iya samun tashin hankali idan wasu suka ce za su fito daukar fansar abin da aka yiwa sarkin.
Majiyar dai ta ce:
"Fusatattun matasa ne suka ci zarafin sarkin, matarsa da kuma dansa. Ba mu san abin da ya jawo hakan ba amma dai matasa ba sa son sarkin, ba mu san dalili ba.
"Idan ba a dauki matakin tsaro da gaggawa ba, lallai wannan lamari na iya rikidewa ya zama babban tashin hankali a gaba daya garin."
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun 'yan sandan Ondo, Olayinka Ayanlade, ya shaida cewa sun fara gudanar da bincike.
"Yanzu haka muna gudanar da bincike kan wannan abu da ya faru kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci."
- Olayinka Ayanlade.

Source: Original
Sarki da Yarima sun yi martani kan harin
Da yake magana da manema labarai, ciki har da Arise News a fadar sarkin, Yarima Victor ya nuna irin raunukan da ya ce matasan sun yi masa.
Yarima Victor ya yi ikirarin cewa maharan sun ci zarafin 'yan gidansu ta hanyar yi wa mahaifiyarsa tsirara, tare da watsa mata fitsari da sauran kayan kazanta, kuma sun bugi sarkin.
Oba Bakare, mai martaba sarki, ya bayyana wannan cin zarafi a matsayin wani 'harin ba gaira ba dalili' da wasu tsagin matasan garin ke ci gaba da kai masa.
Sarkin ya yi Allah-wadai da wannan harin na rashin lissafi, yayin da ya godewa 'yan sanda bisa daukin gaggawa da suka kai, tare da dawo da zaman lafiya a garin.
An kona fadar basarake a Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Borno, inda suka tafka ta'asa.
Miyagun sun hallaka mutum daya tare da kona gidaje da shaguna na mutanen garin Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza a jihar.
Sanata Ali Ndume ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya bukaci gwamnati ta kara tura jami'an tsaro zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


