Fusattatun matasa sun kai hari fadar sarki, sun lakada wa matar sarki duka

Fusattatun matasa sun kai hari fadar sarki, sun lakada wa matar sarki duka

Al'ummar garin llara Mokin da ke karamar hukumar Ifedore na jihar Ondo sun fada cikin rudani a ranar Juma'a sakamakon harin da wasu fusattatun matasa suka kai fadar sarkin garin.

The Punch ta ruwaito cewa al'ummar garin sun yi fushi da Oba Aderemi Adefehinti ne bayan ya ki hallatar wasu bukukuwa na gargajiya da aka gudanar a garin.

Mutane sunyi ikirarin cewa sarkin da ke kan karagar mulki tun 1998 ya dena hallartar bukukuwan gargajiya a garin ne saboda ya canja addini zuwa kiristanci.

Acewar wani wanda abin ya faru a gabansa, rikicin ya barke ne bayan sarkin ya ki hallartar bikin sabon doya inda ya kamata ya yi wasu addu'o'in gargajiya na musamman.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari a kotu: Wani dan PDP ya cakawa dan APC kwalba

Majiyar ta ce, "Matasan sun fusata ne bayan sarkin ya ki hallartar inda ake bikin sabon doyan domin ya yi wasu addu'o'i haka yasa suka kai masa hari a fadarsa suna jifa da duwatsu hakan ya tilasta masa tserewa daga fadar."

Sai dai majiyar ya ce matar sarkin ba tayi sa'ar tserewa ba domin an ce wasu matasa sun lakada mata duka. An ce an garzaya da ita wani asibiti domin yi mata magani.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Femi Joseph ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya ce sarkin da matarsa suna nan lafiya babu abinda ya same su.

Ya ce, "an samu dan rashin jituwa ne tsakanin sarkin da mabiyansa amma ina tabbatar maka da cewa komi da dai-daita a garin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel