Zamfara: Yan Bindiga Sun Dauke Kansiloli, Sun Sace Limami bayan Idar da Sallah
- ’Yan bindiga sun kai wani hari a Tsauni da ke birnin Gusau a jihar Zamfara inda suka sace kansiloli biyu yayin farmakin
- Lamarin ya faru ne da dare inda aka dauke kansilolin biyu daga karamar hukumar Maradun da wani liman bayan sallar Magriba
- Shaidu sun ce maharan sun kwace wayoyin ’yan sanda a bakin ofishinsu ba tare da wata turjiya ba, sannan suka yi gaba da mutanen
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara – Al'ummar jihar Zamfara sun sake cin karo da wani mummunan labari bayan harin yan bindiga kan jama'a.
An tabbatar da cewa yan bindiga sun sace kansiloli biyu da wani liman a harin da suka kai garin Tsauni da ke birnin Gusau.

Source: Facebook
Yadda yan bindiga suka kwace wayoyin yan sanda
Shugaban karamar hukumar Maradun, Sanusi Gama Giwa, ya tabbatar da aukuwar lamarin a sanarwa da jaridar Daily Trust ta samu a yau Alhamis 2 ga watan Octoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi Giwa ya ce mutanen suna zaune a wajen shan shayi lokacin da ’yan bindiga suka farmake su da dare.
Shaidu sun bayyana cewa maharan sun kai harin a gaban ofishin ’yan sanda, inda suka kwace wayoyin ’yan sanda ba tare da wata jayayya ba amma ba su cutar da kowa ba.
Yan bindiga sun sace kansiloli a Zamfara
Rahotanni sun ce kansilolin da aka sace na wakiltar mazabun Gidan Goga da Tsibiri a karamar hukumar Maradun, kuma an kama su ne da misalin ƙarfe 8:05 na dare.
A cewar Giwa, maharan sun fito ne neman wani mutum daga kauyen Kaura,da suka kasa samun shi, sai suka sace mutane shida daga wajen, daga bisani suka sake uku.
Sun ci gaba da tafiya da kansiloli biyu da liman, lamarin da ya kara sanya tsoro a Tsauni, da garin ya dade yana karbar ’yan gudun hijira daga hare-haren ’yan bindiga.

Source: Original
Abin da 'yan sanda suka ce kan harin
Kakakin rundunar ’yan sandan Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya tabbatar da lamarin, ya ce jami’ai sun shiga daji domin gudanar da aikin ceto.
Ya ce ana yin duk mai yiwuwa don kubutar da wadanda aka sace tare da tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Ya kuma roki jama’a da su ci gaba da ba jami’an tsaro bayanai masu amfani da za su taimaka wajen dakile ayyukan ’yan bindiga a jihar, cewar rahoton TVC News.
Makwabcin daya kansilan ya zanta da Legit Hausa
Wani mazaunin yankin Tsibiri ya tabbatar da sace kansilolin da a birnin Gusau da ke jihar Zamfara.
Masa'udu Lawan ya ce tabbas daya daga cikinsu nasu ne kuma ɗan garinsu ne inda ya yi musu addu'o'in neman mafita.
"Eh lallai wadannan kansiloli da aka dauka na Gidan Goga da na Tsibiri, daya na Tsibiri dan garinmu ne, yayana ne kuma makwabcina.
"Suna cikin garin Gusau a wata unguwa da ake kira Tsauni Saminaka wannan jarabawa ta same su, Allah ya yi musu mafita."

Kara karanta wannan
Katsina: Mutane sun yi kukan kura, sun cafke ƴan bindiga da ke taimakon Bello Turji
- Masa'udu Lawan
Zamfara: 'Yan sanda sun kama shedanin dan bindiga
A wani labarin, jami'an rundunar 'yan sandan jihar Zamfara na ci gaba da kokari wajen yaki da 'yan bindiga da masu aikata laifuffuka domin dakile hare-harensu a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Ibrahim Balarabe Maikaba ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da jami'an rundunarsa suka samu.
Daga cikin nasarorin har da cafke wani tantirin dan bindiga da ake zargi da laifin yin garkuwa da mutane da dama a jihar wanda ya shafi mutane da dama a jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

