An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da 'Yan Ta'adda a Taraba, an Samu Asarar Rayuka
- Sojojin rundunar 6 Brigade sun dakile shirin harin ‘yan ta’adda a Taraba, sun halaka mutum biyu tare da kwace makamai da babura
- An yaba wa sojojin bisa yadda suka yi saurin daukar mataki da kwazon da suka nuna wajen kare jama’a daga barazanar ta’addanci
- Sojoji sun bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai don taimakawa ayyukansu na Operation "Lafiya Na Kowa"
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Sojojin rundunar 6 Brigade na Operation Whirl Stroke, sun yi nasarar dakile harin ‘yan ta’adda a kauyen Tor-Ikyeghgba, jihar Taraba.
Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mataimakin daraktan yada labaran rundunar, Laftanal Umar Muhammad ya fitar a ranar Laraba.

Source: Twitter
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Taraba
Laftanal Umar ya bayyana cewa sojojin sun samu nasarar kashe wasu 'yan ta'adda biyu bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
An hallaka shedanin dan bindiga, matasa sun kona fadar Sarki da harsashi ya samu dalibai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bisa amfani da sahihan bayanan sirri, a ranar 1 ga Oktoba, 2025, sojoji suka je kauyen Tor-Ikyeghgba inda aka ce 'yan bindiga sun taru.
"Da zuwansu wajen, sojojin suka yi arangama da 'yan ta'addan a kusa da wani layin wutar lantarki, inda suka yi musayar wuta."
Sanarwar ta ce sojojin sun yi amfani da karfin iya yaki da na makamai wajen dakile yunkurin harin na 'yan ta'addar tare da fatattakarsu.
Laftanal Umar ya ce an kwato makamai da suka hada da bindigar pistol kirar gida, bindigun baushe biyu, harsasai kirar 7.62mm, rediyon Baofeng, babur daya da wasu kayayyaki.
Yabo ga jarumtar sojojin Najeriya
Kwamandan rundunar, Brig. Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa jaruntakar dakarun bisa kwazon da suka nuna da kuma saurin kai daukin da suka yi.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar Taraba cewa rundunar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
Sanarwar ta kara da cewa kwamandan ya bukaci dakarun da su ci gaba da nuna azama, tare da yin kira ga jama’a da su rika bayar da bayanai masu inganci don taimakawa ayyukan sojoji.

Source: Original
Nasarar sojoji a Chanchanji da Takum
Wannan na zuwa ne kwana kadan bayan sojojin 6 Brigade sun fatattaki 'yan ta’adda a karamar hukumar Takum ta yankin Bojo da ke shirin kai hari a kauyen Chanchanji, inji rahoton FRCN.
A cewar sanarwar kakakin rundunar na rundunar, Laftanal Aliyu Danja, sojojin sun yi arangama da mayakan a hanyar Demeva–Chanchanji, inda suka kashe mutum daya sannan sauran suka tsere.
Sojojin sun bi sahun su zuwa Demeva–Gbudu da ke kan hanyar Ananum a karamar hukumar Donga LGA, inda nan ma suka sake kashe wani mutum guda.
'Yan sanda sun gwabza da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar 'yan sanda ta cafke mutane biyu da ake zargin suna cikin kungiyar masu garkuwa da mutane a Bauchi.
An cafke mutanen ne jim kadan bayan da wasu gungun masu garkuwa da mutane suka sace mutane biyu a karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi.
Kwamishinan ’yan sanda, Sani-Omolori Aliyu ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar, yayin da ake ci gaba da neman sauran miyagu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
