Masu Garkuwa da Mutane Sun Ji Azaba, Sun Tsere Daji da Suka Gwabza da 'Yan Sanda
- Rundunar ’yan sanda ta samu nasarar dakile harin garkuwa da mutane a Alkaleri, inda ta ceci mutane biyu da aka sace a Bauchi
- An cafke mutum uku da ake zargi da hannu a harin, kuma sun riga sun amsa laifinsu tare da bayyana abokan harkallarsu uku
- Kwamishinan ’yan sanda, Sani-Omolori Aliyu ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar, yayin da ake ci gaba da neman sauran miyagu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Rana ta baci ga masu garkuwa da mutane, inda suka kwashi kashinsu a hannun jami'an rundunar 'yan sanda a Bauchi.
Rundunar 'yan sandan Bauchi ta ce ta samu nasarar dakile ayyukan masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Alkaleri da kewaye.

Source: Twitter
An kai harin garkuwa da mutane a Bauchi
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa, rundunar ta kuma samu nasarar cafke mutane uku daga cikin wadanda ake zargi sun kai harin.

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri ya yi afuwa ga masu laifi don murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun 'yanci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Bauchi, Ahmed Wakil, ya sanar da batun dakile garkuwa da mutanen a ranar Laraba.
Ahmed Wakila ya sanar da cewa dakile shirin masu garkuwa da mutanen na daga cikin matakan da suke dauka na inganta tsaro a jihar.
A cewarsa, rundunar ta karbi kiran gaggawa a ranar 28 ga watan Satumba, 2025 daga kauyen Maso Kano a gundumar Jada Pali.
'Yan sanda sun fafata da masu garkuwa
Wanda ya yi kiran, ya shaida wa 'yan sandan cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun farmake su da bindigogin AK-47.
An kuma sanar da 'yan sandan cewa miyagun sun yi nasarar awon gaba da mutane biyu, wani Hambali Alh. Sa’adu, dan shekara 50, and Jari Alh. Sa’adu, dan shekara 35.
The Nation ta rahoto Ahmed Wakil ya bayyana cewa rundunar hadin gwiwa ta 'yan sanda da mafarauta ta kai daukin gaggawa, inda ta sha gaban 'yan ta'addar.
Ya ce an yi musayar wuta mai zafi, kuma masu garkuwa da mutanen suka ji azaba, suka tsere daji tare da kyale wadanda suka sace.
"Wadanda aka sacen suna nan cikin koshin lafiya, kuma ana kan kokarin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki."
- Ahmed Wakil.

Source: Original
Bauchi: An cafke masu garkuwa da mutane
Ahmed Wakil ya ce yayin bincike tsakanin Litinin zuwa Talata, rundunar ta cafke mutum uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Alkaleri da Kirfi.
Wadanda aka cafke din su ne: Adamu Ahmadu dan shekara 28, Bello Alhaji Musa dan shekara 18 da Adamu Alhaji Musa dan shekara 29.
Ya ce dukkanin wadanda aka kaman sun fito ne daga kauyen Shalhori da ke kusa da Kirfi, kuma sun amsa laifinsu, tare da cewa sun hada baki ne da wasu mutum uku da yanzu ake nemansu.
Ahmed Wakil ya ce kwamishinan 'yan sandan Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya jinjinawa jami'an da suka yi namijin kokari wajen dakile garkuwa da mutanen.
'Yan bindiga sun sace mutum 26 a Bauchi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Alkaleri, jihar Bauchi inda suka sace mutane 26.
Wani mazaunin kauyen Gale ya ce 'yan bindigar sun bude wuta kan mai uwa da wabi, kuma sun kashe mutum daya bayan sace mutanen 26.
Iyalan wadanda aka sace sun biya N1.5m domin kuɓutar da ɗaya daga cikin su, yayin da ragowar mutanen ke hannun miyagun.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

