Akpabio Ya Yi Wa Shugaba Tinubu Albishir kan Zaben 2027
- Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya sanar da Mai girma Bola Tinubu abinda bai sani ba kan shirin wasu gwamnonin jam'iyyun adawa
- Sanata Godswill Akpabio ya gayawa shugaban kasan cewa wasu gwamnonin jam'iyyun adawa sun shirya dawowa cikin jam'iyyar APC
- Shugaban majalisar dattawan ya kuma bayyana cewa 'yan Najeriya sun fara gani a kasa kan manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Imo - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi albishir ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Godswill Akpabio ya bukaci Shugaba Tinubu ya shirya tarbar karin gwamnonin jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki kafin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikita wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Jackson Udom, ya fitar.
Ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da littafi mai taken “Shekaru 10 na jagoranci mai tasiri na gwamnatin APC a Najeriya” wanda Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya rubuta.
Me Akpabio ya gayawa Tinubu?
Akpabio ya ce akwai wasu gwamnonin da ke kammala shirye-shiryensu domin shiga APC, inda ya jaddada cewa ‘yan Najeriya sun riga sun fara ganin amfanin manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.
"Mai girma shugaban kasa, bisa irin abin da ka yi cikin shekaru biyu da suka gabata, ka shirya don karɓar karin gwamnonin jam’iyyun adawa."
"A yanzu da nake magana, akwai gwamnoni da dama a Najeriya da suka shirya shiga APC."
- Godswill Akpabio
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa 'yan Najeria sun fara ganin amfanin manufofin da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
"Dalibai, manoma da ‘yan kasuwa sun fara magana a kan manufofin da ka kawo a cikin gwamnati, waɗanda yanzu sun fara haifar da sakamako mai amfani ga al’umma."
"Idan mu ne muka faɗa, za su zarge mu da cewa muna zuzuta nasarorinka, amma waɗanda suka amfana kai tsaye sune suke bayyanawa a fili abin da ka yi. Ni na yi amanna da samar da ci gaba mai dorewa."
- Godswill Akpabio

Source: Facebook
Akpabio ya godewa Gwamna Uzodinma
Hakazalika shugaban majalisar dattawan ya godewa Gwamna Uzodimma saboda rubuta littafin.
"Na godewa Gwamna Uzodimma bisa saka tarihi a rubuce cikin littafin shekaru 10 na jagoranci mai tasiri na gwamnatin APC a Najeriya. Domin idan ba ka faɗi labarinka ba, wasu za su faɗa maka shi ta yadda suka ga dama."
- Godswill Akpabio
Tinubu ya sake tabo batun cire tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake yin magana kan batun cire tallafin man fetur da ya yi bayan hawa kan karagar mulkin Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa wajibi ne ya tilastawa gwamnatinsa cire tallafin fetur, duk da matakin ya kasance ba mai sauki ba.
Mai girma shugaban kasan ya tabbatar da cewa cire tallafin man ya mayar da dukiyar kasa ga jama'a, tare da ceto kasar nan daga rugujewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

