Dalilin Gwamna Abba na Raba wa Matasa 5,384 Tallafin Naira Miliyan 807 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon tallafin matasa a Kano, inda mutane 5,384 suka samu jarin N150,000 kowanne
- An kawo shirin ne don tallafawa matasa wajen fara sana’o’in dogaro da kai, yayin da aka ba wasu kudin don fadada kasuwancinsu
- Gwamna Abba ya ba da hakuri ga wadanda ba su samu damar da shiga cikin kashin farko na shirin ba, inda ya daukar masu alkawari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da rabon N150,000 ga matasa a matsayin matakin farko na shirin KSYEP.
Shirin KSYEP dai an tsara shi domin baiwa matasa damar fara sana’o’i ko kuma faɗaɗa harkokin kasuwancinsu ta hanyar ba su tallafin kudi.

Source: Twitter
Abba ya rabawa matasa N150,000 a Kano
A sanarwar da ya fitar a shafisa na X, Gwamna Abba ya sanar da cewa matasa 5,384 - maza da mata ne suka amfana da kashin farko na shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an raba wa kowanne matashi N150,000 domin gina kasuwanci ko kuma fadada kasuwancin da yake yi a lokacin.
Gwamna Abba Yusuf ya ce:
"A yau, mun dauki wani babban mataki na bunkasa matasanmu ta hanyar kaddamar da kashin farko na shirin tallafawa matasan Kano (KSYEP).
"An samar da wannan shirin ne domin tallafawa matasanmu da ke harkokin kasuwanci ta hanyar ba su kudin fadada kasuwancin, da wadanda ke farawa yanzu.
"A wajen taron, na bayyana cewa matasa 5,384, maza da mata ne suka samu tallafin N150,000 kowannensu."
Dalilin Abba na tallafawa matasa da N150,000
Rahoto ya nuna cewa an kaddamar da shirin ne a ranar Talata a Kano, a wani bangare na kokarin gwamnatin Abba na magance matsalar rashin ayyuka da koma sa matasa su dogara da kansu.
Gwamna Abba ya ce an samar da shirin don bunkasa matasa da jarin da suke bukata, wanda zai sanya su zamo daga cikin masu gina tattalin Kano.
"Wannan shirin zai taimakawa matasanmu su zamo daga cikin 'yan jihar da ke harkokin kasuwanci, wanda zai taimaka wajen ci gaban al'umma."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Source: Twitter
Gwamna ya yi magana da matasan Kano
Ya bukaci wadanda suka samu tallafin da su yi amfani da tallafin kudin yadda ya kamata don faɗaɗa sana’o’insu da kuma gina kyakkyawar makoma.
Haka kuma, gwamnan ya roƙi waɗanda ke cikin jerin jiran tallafi na gaba da su yi hakuri, yana mai tabbatar da cewa za a yi rabon tallafin kashi na biyu nan ba da jimawa ba.
Gwamna Abba ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da shirye-shirye da tsare-tsare da za su fifita ci gaban matasa, samar da ayyuka da walwalar jama'ar Kano.
Gwamna zai nada sababbin kwamishinoni
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aika da sunayen wasu mutane ga majalisar dokoki don nada su kwamishinoni.
Abba Kabir Yusuf ya mika sunayen ne ga majalisar domin tantancewa da tabbatarwa a matsayin kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa.

Kara karanta wannan
Kwamishinan 'yan sanda ya fusata Gwamna Abba a wurin faretin ranar 'yancin kai a Kano
Mutanen biyu suna da kwarewa a fannonin da su ke aiki, kuma sun fito ne daga kananan hukumomin Bichi da Minjibir kamar yadda rahoto ya nuna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

