Kano: Ganduje zai gina wata gaggarumin cibiyar kasuwanci a Kana mafi girma a Najeriya (Hotuna)
- Gwamnatin jihar Kano za ta gina wata gaggarumin cibiyar kasuwanci mafi girma a yankin arewa a Kano
- Za a gina cibiyar a Dangwauro da ke a kan hanyar Zaria da hadin gwiwar kamfanin Brain & Hammers
- Gwamna Ganduje ya ce idan aka kammala cibiyar, zai samar wa matasa miliyan daya ayyukan yi
Aikin gina cibiyar kasuwanci wato Kano Economic City (KEC) wanda gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Ganduje tare da haɗin gwiwar kamfanin Brain & Hammers ke ginawa yanzu a garin Dangwauro da ke a kan hanyar Zaria ta yi nisa.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, wannan cibiyar kasuwanci na daya daga cikin shirin gwamna Ganduje wanda bayan kammalawa zai taimaka da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Kano ta hanyar kawo kai tsaye masu zuba jari daga nan gida har kasashen waje.
KU KARANTA: Wata kungiyar dalibai ta kai karar gwamnatin jihar Kaduna
A cewar gwamnan cibiyan kasuwancin (KEC) zai kuma taimaka wajen samar wa matasan jihar fiye da miliyan daya ayyukan yi. Idan aka kammala cibiyar zai kasance ya fi kasuwar Wuse da Asokoro da ke birnin Abuja girma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng