Abin Kunya: Malamin Addini Ya Yaudari Yar'uwa da Ƙanwarta a Wurin Ibada, Ya Auka Musu

Abin Kunya: Malamin Addini Ya Yaudari Yar'uwa da Ƙanwarta a Wurin Ibada, Ya Auka Musu

  • Dubun wani malamin addinin Kirista ya cika bayan cafke shi da cin amana yayin wa'azi a cocinsa
  • An tura Faston mai shekara 63, Luke Eze, gidan yari bayan an tuhume shi da cin zarafin ’yan mata biyu a Enugu
  • Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa ya yaudari yaran masu shekara 16 da 19 zuwa coci sannan ya batar musu da hankali

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Enugu - An tasa keyar wani Fasto dan shekara 63 mai suna Luke Eze gidan yari bayan aikata abin kunya a jihar Enugu.

Ana tuhumar shi da aukawa wa ’yan mata biyu wadanda ’yan uwan juna ne a jihar Enugu da ke Kudancin Najeriya.

Fasto ya aukawa mata 2 yan gida daya
Taswirar jihar Enugu da ke Kudu maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Fasto ya shiga hannun yan sanda a Enugu

Rahoton Punch ya ce iyayen yaran sun kai ƙara, inda aka cafke faston a ranar 11 ga Satumba 2025, bisa zarginsa da laifin cin zarafin adda da kanwarta.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

Kakakin ’yan sandan jihar Enugu, SP Daniel Ndukwe, ya ce Faston ya jawo yaran zuwa cocinsa na 'City of Hope Ministry' don “yi musu wa'azi” a ranar 7 Satumba.

Ya ce:

“Ya tilasta mata yin wasu abubuwa, sannan ya ba ta wani abin sha da ya sa ta suma, ya yi mata fyade."

Yadda Faston ya ci zarafin 'yan matan

Bayan ƙaramar yarinyar ba ta dawo gida ba, babbar ’yar shekara 19 ta bi ta zuwa coci, inda aka maimaita mata irin wannan dabarar yaudara.

Ndukwe ya ce Faston ya ba kowannensu kayan maye, ya bar su sumammu, sannan ya ci zarafisu, kafin su farfaɗo washegari ba tare da tufafi ba.

“Dukkaninsu sun farfaɗo washegari suna tsirara da jini a al’aurarsu da sauran hujjoji da aka samu na tashin hankali."
An kama Fasto kan cin zarafin adda da kanwa a Enugu
Babban Sufetan yan sanda a Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Twitter

Matakin yan sanda kan Fasto a Enugu

Ya ce Faston ya amsa laifinsa, yana cewa “shaidan ne ya sanya shi,” kuma an kwato kwalaben kayan maye domin bincike a dakin gwaje-gwaje.

Kara karanta wannan

"A fito da rahoto": Otedola ya fusata kan zarginsa da badakalar tallafin mai

Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa an gurfanar da shi a kotu bayan kammala binciken sashe na 'Gender and Anti-Human Trafficking' na CID.

“Kwamishinan ’yan sanda, CP Mamman Bitrus Giwa, ya ce wannan aiki abin ƙyama da rashin hankali ne, ya gargadi jama’a su yi hattara da masu ikirarin malanta.”

Ndukwe ya ƙara da cewa, “Kwamishina ya tabbatar wa jama’a cewa za a tabbatar da adalci a wannan lamari,” inda ya jaddada ƙudurinsu na kare al’umma.

An kama Fasto da ke aukawa yarsa

Mun ba ku labarin cewa mutane sun shiga wani irin yanayi bayan cafke malamin addinin da ke cin zarafin yarsa har na tsawon lokaci ba kakkautawa.

Faston mai shekaru 42, Samson Ajayi, ya shiga hannun hukuma bayan ya amsa laifin aukuwa ‘yarsa na tsawon shekaru hudu wanda ya illata mata rayuwa gaba daya.

A cewar lauyan gwamnati, laifin ya faru a kai-a kai daga 2021 zuwa 2025 a Igoba, kuma ya sabawa dokokin hana cin zarafi na Ondo inda ya tabbatar da daukar mataki kan mutumin da ake zargi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.