Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Yi Jawabi Kai Tsaye ga 'Yan Najeriya

Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Yi Jawabi Kai Tsaye ga 'Yan Najeriya

  • Najeriya za ta yi bikin cika shekaru 65 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka a gobe Laraba, 1 ga Oktoba, 2025
  • An shirya Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya a ranar Laraba da misalin karfe 7:00 na safe
  • An umurci dukkan gidajen talabijin, rediyo, da sauran kafafen yada labarai da su kama NTA da FRCN domin watsa jawabin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A gobe Laraba, 1 ga watan Oktoba ne Najeriya ke cika shekaru 65 da samun 'yanci daga mulkin Turawan Mallaka.

Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa cewa, Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya a ranar Laraba
Shugaba Bola Tinubu a tsaye yayin da ake shirin fara taron FEC a fadar shugaban kasa. Hoto: @tinubu
Source: Twitter

Bola Tinubu zai yi jawabi kai tsaye

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na X a daren ranar Talata, 30 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Ganduje ya hadu da shugaban kasa, Tinubu ya magantu kan zargin kisan Kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Bayo Onanuga ya ce shugaban kasar zai yi jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya a safiyar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025.

Wannan jawabi na Shugaba Bola Tinubu zai shafi batutuwan da suka shafi Najeriya daga lokacin samun 'yancin kai zuwa yanzu.

Fadar shugaban kasa ta bukaci daukacin gidajen rediyo, talabijin, da kafofin watsa labarai su watsa jawabin Tinubu kai tsaye.

An ba kafofin watsa labarai umarni

Kafofin watsa labaran za su iya watsa jawabin kai tsaye ne ta hanyar bibiyar gidan talabijin na NTA kai tsaye, da kuma gidan rediyon tarayya na FRCN.

Sanarwar Bayo Onanuga ta ce:

"Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan kasa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba, 2025 da misalin karfi 7:00 na safiya domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun 'yanci.
"An umarci dukkan gidajen talabijin, rediyo, da sauran dangogin kafafen yada labarai da su haɗa da’ira da NTA da FRCN domin watsa jawabin kai tsaye."

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 da ya kamata jam'iyyar ADC ta yi don kayar da Tinubu, APC a zaben 2027

Bikin ranar samun 'yancin kai

Ranar ‘yancin kai rana ce ta hutu a Najeriya da aka ware duk shekara a ranar 1 ga Oktoba domin tunawa da samun ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1960.

Ana gudanar da bikin ranar ne a fadin kasa baki daya, ta hanyar bukukuwan gwamnati, jerin rawar dajin sojoji, nuna al’adun gargajiya da tarukan jama’a.

Wannan rana ta samo asali ne daga ci gaban tsarin mulki da Najeriya ta samu a karkashin mulkin mallakar Turawan Birtaniya, cewar wata wallafa a shafin WikiPedia.

An fara bikin ranar 'yancin kan Najeriya da misalin karfe 12:00 na daren 1 ga Oktoba, 1960
Hoton 'yar Najeriya rike da tutocin Najeriya masu launin kore-fari-kore a ranar 'yancin kai. Hoto: Andrii Kalenskyi, Adekunle Ajayi
Source: UGC

Abin da ya faru a ranar 1 ga Oktoba, 1960

Bayan zaben tarayya na 1959, gwamnatin hadin gwiwa karkashin jagorancin Abubakar Tafawa Balewa ta jagoranci kasar zuwa samun ‘yancin kai.

Da karfe 12:00 na daren ranar 1 ga Oktoba, 1960, aka sauke tutar Birtaniya (Union Jack) a Legas, aka daga tutar Najeriya mai launin kore–fari–kore.

Sarauniya Alexandra na Kent, wacce ta wakilci Sarauniya Elizabeth II, ta mika takardun tsarin mulkin ‘yancin kai, aka rantsar da Nnamdi Azikiwe a matsayin babban gwamna, sannan shugaba Abubakar Tafawa Balewa ya gabatar da jawabin kasa.

Kara karanta wannan

Abuja ta zama abin tsaro, Tinubu ya ba da umarni bayan yi wa yar jarida kisan gilla

Gwamnati ta ba da hutun kwana 1

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da hutun kwana daya domin bikin zagayowar ranar 'yancin kan kasar.

A cikin wata sanarwa, ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa za a yi hutun ne a ranar 1 ga Oktoba, 2025.

Ministan ya roƙi ’yan Najeriya da su ci gaba da rungumar kishin ƙasa, haɗin kai da juriya, wadanda ke goye da Najeriya tun daga samun ’yancin kai a 1960 zuwa yau.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com