Abuja Ta Zama Abin Tsaro, Tinubu Ya ba da Umarni bayan Yi wa Yar Jarida Kisan Gilla

Abuja Ta Zama Abin Tsaro, Tinubu Ya ba da Umarni bayan Yi wa Yar Jarida Kisan Gilla

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wata fitacciyar yar jarida a birnin tarayya, Abuja
  • Tinubu ya jajanta wa iyalan marigayiya Somtochukwu Maduagwu, mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin Arise News
  • Ya umurci jami’an tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa don kamo wadanda suka aikata wannan mummunan aiki kan matashiyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana takaicinsa kan kisan gilla da aka yi wa fitacciyar yar jarida a Abuja.

Wasu yan fashi sun hallaka Somtochukwu Maduagwu, mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise News.

Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni a Abuja
Shugaba Bola Tinubu da yar jaridar Arise News da aka kashe. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya kadu bayan kisan yar jarida

Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X a yau Talata 30 ga watan Satumbar 2025.

Kara karanta wannan

Batanci: Malaman Izala sun yi zama kan maganar 'sakin' Abduljabbar Nasiru Kabara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar cewa Somtochukwu Maduagwu ta rasu sakamakon farmakin ‘yan fashi a gidanta da ke Katampe a birnin tarayya da ke Abuja.

Sanarwar ta ce:

“Shugaban kasa ya bayyana marigayiya Somtochukwu, wacce aka fi sani da Sommie, a matsayin kwararriya mai tasowa da aka katse rayuwarta ta hanyar zalunci mai ban takaici.”

Sakon da Tinubu ya tura ga iyalan marigayiyar

Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Maduagwu, shugabanci da ma’aikatan Arise News, da kuma dukkan al’umma da ‘yan jarida a Najeriya, yana mai cewa wannan asara ta shafi kasa baki daya.

Ya kuma umurci hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da tabbatar da cewa an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin a hukunta su.

Shugaban kasar ya sake nanata kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Ya tabbatar da cewa za a kara daukar matakai don shawo kan aikata miyagun laifuffuka a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Tinubu ya kadu bayan kashe yar jarida a Abuja
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a birnin Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da abokan aikin 'yan jaridar ke cewa

Tashar Arise News ta tabbatar da mutuwar Maduagwu, wacce abokan aikinta suka bayyana cewa ta rasu ne bayan ta samu raunuka daga farmakin ‘yan fashi, amma aka ki karbar ta a asibiti.

Ojy Okpe da Reuben Abati, abokan aikinta a The Morning Show, sun ce mutuwarta abu ne da za a iya kauce masa tun da wuri.

Sun kuma jaddada cewa kin amincewar asibiti ya taimaka wajen rasa rayuwar matashiyar da ke da himma a wurin aiki.

“Ta dura daga gidanta bayan jin cewa ‘yan fashi 14 sun mamaye gidan. Duk da cewa ta tsira daga faduwar, daga bisani ta rasu saboda kin karbar ta a asibiti. Wannan babban abin takaici ne."

Cewar Okpe

Tinubu ya magantu kan halin kunci

Kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya ke shan wuya a gwamnatinsa

Tinubu ya nuna cewa tattalin arzikin kasar nan ya fara farfadowa saboda matakan da gwamnatinsa ta dauka wanda za a ci moriya nan gaba kadan.

Shugaban kasan ya godewa 'yan Najeriya bisa hakuri da juriyar da suka nuna sakamakon sauyin da aka samu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.