Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Ke Shan Wuya a Gwamnatinsa

Shugaba Tinubu Ya Fadi Dalilin da Ya Sa 'Yan Najeriya Ke Shan Wuya a Gwamnatinsa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki
  • Mai girma Tinubu ya nuna cewa tattalin arzikin kasar nan ya fara farfadowa saboda matakan da gwamnatinsa ta dauka
  • Shugaban kasan ya godewa 'yan Najeriya bisa hakuri da juriyar da suka nuna sakamakon sauyin da aka samu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kwatanta matsin tattalin arziki da ya biyo bayan wasu daga cikin manufofin gwamnatinsa da radadin da ake ji bayan an yi tiyata.

Shugaba Tinubu ya ce tattalin arzikin Najeriya na murmurewa daga matsalolin da ya fuskanta, tare da godewa ‘yan kasa bisa juriya da hakurin da suka nuna.

Shugaba Tinubu ya magantu kan matsin tattalin arziki
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Bola Tinubu ya halarci nadin Olubadan

Jaridar Vanguard ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a dakin taro na Mapo, IIbadan, jihar Oyo, yayin bikin nadin Oba Rashidi Adewolu Ladoja a matsayin Olubadan na Ibadan na 44.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya hadu da Kwankwaso gaba da gaba, an ga abin da ya faru a bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya isa wurin ne tare da Gwamna Seyi Makinde da misalin karfe 2:28 na rana.

A cikin tawagarsa akwai gwamnonin jihohin Ondo, Osun, Ekiti da wasu mambobi na majalisar zartaswa ta tarayya.

An nada basaraken a matsayin Olubadan na Ibadan na 44 kafin zuwan shugaban kasan.

Me Tinubu ya gayawa 'yan Najrleriya?

Shugaban kasan ya nuna godiyarsa ga ‘yan Najeriya da suka zaɓe shi a shekarar 2023, yana mai cewa tattalin arzikin kasar nan ya fara farfadowa.

"Yau, ina alfaharin sanar da cewa tattalin arziki ya fara murmurewa, akwai alamun nasara."
"Wahalar da kuke sha radadi ne na tiyata mai zafi, amma ya dawo da damar ci gaba da wadata da ke jiranmu. Na gode bisa juriya, hakuri da fahimta."

- Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Tun daga hawansa mulki a 2023, gwamnatin Tinubu ta aiwatar da wasu manufofi, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma daidaita kasuwar canjin kuɗi.

Kara karanta wannan

Sarki ya kinkimo bukatar kirkiro jiha 1, ya fadawa Tinubu gaba da gaba a Ibadan

Cire tallafin man fetur ya haddasa tashin kuɗin sufuri da farashin kayayyakin abinci na yau da kullum.

Shugaba Tinubu ya godewa 'yan Najeriya
Hoton shugaban kasan Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Manyan mutane sun halarci nadin Olubadan

Bikin nadin ya samu halartar manyan shugabannin siyasa da na gargajiya. Cikin gwamnoni da suka halarta akwai Lucky Aiyedatiwa na Ondo, Ademola Adeleke na Osun, da Biodun Oyebanji na Ekiti, rahoton TheCable ya tabbatar da labarin.

Sauran manyan baƙi sun haɗa da ministan lantarki, Adebayo Adelabu, shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji, tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakazalika, sarakunan gargajiya da suka halarta sun haɗa da Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, da Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Owoade.

Shugaba Tinubu ya hadu da Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hadu da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan 'yan siyasa

Shugaba Tinubu ya hadu da manyan mutanen ne a wajen bikin nadin Olubadan Ibadan na 44, Oba Rashidi Ladoja, a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamna ya zama Sarki mai martaba a Najeriya

Mai girma Tinubu ya hadu da Kwankwaso inda suka gaisa a wurin nadin sarautar da aka yi wa tsohon gwamnan na jihar Oyo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng