Asiri Ya Tonu: Dakarun Sojoji Sun Cafke Masu Hada Baki da 'Yan Ta'adda a Katsina
- Dubun wasu masu hada baki da 'yan ta'adda ta cika bayan sun fada komar jami'an tsaro a jihar Katsina
- Dakarun sojoji tare da hadin gwiwar jami'an rundunar C-Watch sun samu nasarar cafke mutanen da ake zargi bayan gudanar da bincike
- Hakazalika, sojojin sun kuma samu nasarar ceto wani mutum da 'yan ta'adda suka dauke yana tsaka da aiki a gonarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Fansan Yanma tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar C-Watch, sun cafke wasu mutane a Katsina.
Dakarun sojojin sun kama mutanen ne bisa zargin hada baki da ‘yan ta’adda a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun cafke masu hada baki da 'yan ta'adda
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa waɗanda aka kama sun haɗa da mai samar da kayan aiki, Aminu Rabiu Zango, mai shekara 52, da kuma wani mai ba ‘yan ta’adda bayanai, Alhaji Abdulrahman Tambaya, mai shekara 52.
"Aminu Rabiu Zango ya amsa cewa ɗansa ne ke kai wa shugaban ‘yan ta’adda Babaru makamai da alburusai, kuma kwanan nan ya koma Karu a Abuja."
"Haka kuma ya amsa cewa yana aiki ne karkashin Alhaji Iliya Zango, wanda ake cewa shi ne na gaba da Babaru."
"Alhaji Abdulrahman Tambaya kuma an same shi da ɗaya daga cikin lambobin wayar da Babaru ke amfani da su a wayarsa."
- Wata majiya
Majiyar ta kara da cewa wani da ake zargin yana samar da kayan aiki, Ado Dan Zaria, ya tsere ta hanyar tsallaka katangar gidansa lokacin da sojoji suka iso.
Jami'an tsaro sun gudanar da bincike a gidansa sannan daga bisani aka rushe shi.
Sojoji sun ceto mutumin da aka sace
Haka kuma, dakarun sojojin sun ceto wani mutum da aka sace a karamar hukumar Kankara.
Mutumin da aka ceto mai suna Mallam Yakubu Abdullahi, mai shekara 55, yana sana'ar sayar da shayi.

Source: Original
An samu nasarar ceto shi ne a tsaunukan Zango bayan ya tsere daga hannun ‘yan ta’adda.
"An sace shi ne a ranar 27 ga Satumba tare da wasu mutane biyu a gonarsu da ke hanyar Bagoma a Kankara. Ya samu damar tserewa yayin da ‘yan ta’addan suka gudu cikin duwatsu tare da sauran mutanen da suka sace."
- Wata majiya
Majiyar ta kara da cewa an tantance bayanan wanda aka ceto, kuma nan ba da jimawa ba za a haɗa shi da iyalansa.
Jami'an tsaro sun dakile harin 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Danja, inda suka yi yunkurin yin garkuwa da wasu mutane.
Sai dai, jami'an tsaro sun yi artabu da su, inda suka samu nasarar hallaka daya daga cikinsu tare da kubutar da mutanen da suka yi yunkurin sacewa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


