Girma Ya Fadi: Basarake Ya Rasa Sarauta kan Zargin Satar Tiransifoma 2
- Wani mai rike sarautar gargajiya ya rasa kujerarsa bayan zarginsa da satar injunan wutar lantarki a jihar Osun
- Oba Clement Adesuyi Haastrup Ajimoko III, Owa Obokun na Ijesa, ya tsige Busuyi Gbadamosi, bisa zargin da ake yi masa
- An ce shugaban ya kasa maido da injunan duk da umarnin fada da shawarwarin kwamitin sasanta rigingimun sarauta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ilesa, Osun - Rundunar yan sanda a jihar Osun ta tabbatar da kama basarake kan zargin satar injunan wutar lantarki.
Oba Clement Adesuyi Haastrup Ajimoko III, Owa Obokun na Ijesa, ya tsige daya daga cikin masu sarautar gargajiya, Busuyi Gbadamosi, bisa zargin satar injunan wutar lantarki guda biyu na al’umma.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da dan gidan sarautar Ijesa, Isaac Haastrup wanda kuma dan jarida ne ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Zargin da ake yi wa basaraken a Osun
Sarkin ya bayyana cewa an dauke injunan masu karfin 300KVA da 500KVA ne a shekarar 2023 lokacin mulkin marigayi Oba Gabriel Adekunle Aromolaran.
Shugabannin al’umma sun tabbatar da cewa Gbadamosi ya cire injunan da dare, sannan ya yi ƙoƙarin rufe laifinsa ta hanyar ba da kuɗi.
Lokacin bincike, Gbadamosi ya amsa cewa ya sayar da injin mai karfin 300KVA kan N120,000 kuma ya kai ɗayan Ibadan wai domin gyara.
Duk da bai cika wa’adin kwanaki 30 da aka ba shi ba, da ƙarin kwanaki bakwai, Oba ya tsige shi daga matsayin Oba-Odo na Ilesa.
Oba ya umarci jama’a su guji kiransa da suna Oba-Odo, tare da barin gidan sarauta, domin kare darajar masarautar Ijesa.
Biyo bayan ƙin bin umarni, Owa Obokun ya ƙara wa Gbadamosi kwanaki bakwai. Amma da bai cika wa’adin ba, Sarki ya umarci tsige shi daga mukamin sa.
Sanarwar ta ce:
“Daga yau, Chif Busuyi Gbadamosi ba za a sake kiransa da Oba-Odo na Ilesa ba, ya gaggauta barin gidan sarauta da ke kulle.”

Source: Original
Gargadin da aka yiwa jama'a kan basaraken
An sanar da jama’a cewa ka da su sake kiran ko mu’amala da shi a matsayin Oba-Odo, Sarkin ya ce an ɗauki matakin kare al’adar Ijesa ne.
Mutane da dama sun yi ta magana kan dalilin tube shi ba tare da kammala bincike ba inda suke ganin ya kamata a ba shi dama domin kare kansa game da zargin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta tabbatar da kama shi kan zargin satar injunan, inda aka ce bincike kan lamarin yana ci gaba da gudana.
Ana zargin kansila, basarake da satar transifoma
A wani labarin, dubun wasu manya a cikin al'umma ta cika bayan cafke su da zargin satar tiransifomar wutar lantarki a jihar Gombe.
Rundunar ƴan sanda ta yi nasarar cafke kansila da kuma dagacin kauyensu kan zargin sata da kuma siyar da tiransifoma.
Kakakin rudunar 'yan sanda a Gombe, ASP Buhari Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin da halin da ake ciki bayan zarginsu da almundahana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


