Babban Sarki Ya Rasu a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Taka Har Fada Yin Ta’aziyya
- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kai ziyara ta ta’aziyya ga dangin marigayi Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Kayode Adetona
- Sarkin Musulmi ya fara da ziyartar kabarin marigayin inda ya yi addu’a don samun Aljanna Firdausi, kafin tarbar girmamawa daga manyan Ijebu
- Sarakunan Ijebu da iyalan marigayin, ciki har da matansa da ‘ya’yansa, sun tarbi Sarkin Musulmi cikin girmamawa tare da nuna godiya sosai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Ijebu, Ogun - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kai ziyara ta ta’aziyya bayan mutuwar babban Sarki a Najeriya.
Sultan ya tashi musamman zuwa masarautar Ijebu domin ta'aziyya ga iyalan marigayi Awujale na Ijebu, Oba Sikiru Adetona.

Source: Facebook
Sarkin Musulmi, wanda ya halarci karramawar Rashidi Adewolu Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan, ya ziyarci dangin Adetona a Ogun, cewar NTA News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasuwar Sarki da Buhari ta tayar da hankali
Marigayi ya rasu ranar Lahadi 13 ga Yuli, 2025 da shekarunsa 91, a rana daya da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Buhari ya rasu ne a birnin London bayan ya yi fama da jinya na wani lokaci wanda mutuwarsa ta gigita yan Najeriya.
Fadar shugaban kasa ta umarci Kashim Shettima ya yi gaggawar zuwa birnin London domin dawo da gawarsa zuwa Najeriya.
Abin da Sarkin Musulmi ya ce kan marigayin
A jawabinsa Sultan ya yi godiya ga Ubangiji bisa ni'imomin da ya yi musu na haduwa a wannan rana tare da yiwa marigayin addu'o'i.
Ya ce:
“Da farko, muna gode wa Allah Maɗaukaki bisa ni’imominsa da kuma haɗa mu a wannan rana a matsayin iyali guda, Na ce iyali guda domin ni ma na cikin dangin Awujale.
"Muna gode wa Allah Maɗaukaki da ya kawo mu gida, kuma da zuwanmu kai tsaye muka nufi kabarin ɗan’uwanmu, abokinmu, inda muka yi masa addu’a, duk da muna yi masa addu’a tun yana raye, da lokacin da yake gudanar da ayyukansa, har lokacin da Allah Maɗaukaki ya kira shi. Muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya gafarta masa kuma Ya ba shi Aljannatul Firdaus.”

Source: Facebook
Tarbar da Sarkin Musulmi ya samu a fadar Ijebu
Rahoton Punch ta ce an karɓe Sultan da tarba mai kyau daga manyan shugabannin Ijebu ciki har da regent, Olor’ogun Dr. Sonny Folorunso Kuku, da Dr. Kunle Hassan.
Haka kuma matan marigayin biyu, Olori Agba Iyabode Adetona da Olori Modupe Adetona sun halarta, yayin da Olori Obakemi ba ta samu damar zuwa ba.
‘Ya’yan marigayin ciki har da Prince Ademola Adetona, Prince Adeniyi da Princess Adetoun suma sun tarbi Sarkin Musulmi cikin girmamawa.
Murna a fadar Ijebu kan ziyarar Sarkin Musulmi
A jawabinsa, Regent Sonny Kuku ya ce abin farin ciki da alfahari ne tarbar Sarkin Musulmi guda a fadar.
Ya ce:
"Wannan abin alfahari ne da kuma mutuntawa, ina mika sakon gaisuwa na musamman da kuma yi maka maraba zuwa wannan fada.“
Ya kara da cewa zuwan Sarkin Musulmi shaida ce ta karfin zumunci da ‘yan’uwa tsakanin al’ummominsu duk da matsananciyar jadawalin ayyukansa.
Bayan rasuwar Buhari, babban Sarki ya mutu
Mun ba ku labarin cewa kwana daya da rasuwar Muhammadu Buhari, Najeriya ta sake shiga alhini yayin da sarkin Ijebu, Sikiru Adetona, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.
Gwamna Dapo Abiodun wanda ya tabbatar da rasuwar sarkin, ya marigayin ya taimaka wajen gina kasar Ijebu da ma jihar Ogun.
Oba Adetona ya dare karagar sarauta a 1960, ya yi mulki tsawon shekaru 65, kuma ya inganta kasarta ta fuskar ilimi, lafiya da sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


