Mai Martaba Sarki Ya Kinkimo Bukatar Kirkiro Jiha 1, Ya Fadawa Tinubu Gaba da Gaba a Ibadan

Mai Martaba Sarki Ya Kinkimo Bukatar Kirkiro Jiha 1, Ya Fadawa Tinubu Gaba da Gaba a Ibadan

  • Sarkin Ibadan da aka nada yau Juma'a, Rashidi Ladoja ya roki Bola Tinubu ya raba jihar Oyo zuwa jihohi biyu kafin zaben 2027
  • Olubadan na 44 ya yi wannan roko ne a wurin bikin nadinsa da Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan kasar nan suka halarta
  • Majalisar Tarayya na ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen kara jihohi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Jim kadan bayan hawa kan sarauta a hukumance, Olubadan na 44, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, ya yi kira da a kirkiro jihar Ibadan daga cikin Oyo.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga al’ummar Ibadan bayan karɓar sandar mulki daga hannun Gwamna Seyi Makinde a dakin taro na Mapo Hall.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, tsohon gwamna ya zama Sarki mai martaba a Najeriya

Shugaba Tinubu tare da Olubadan.
Hoton Shugaba Tinubu tare da Olubadan na 44 da Gwamna Makinde a wurin bikin nadin Sarkin Ibadan Hoto: Sunday Dare
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin nadin sabon Sarkin na Ibadan a yau Juma'a, 26 ga watan Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olubadan ya roki kafa jihar Ibadan kafin 2027

Da yake jawabi ga dubunnan mutanen da suka halarci bikin, Olubadan na 44 ya roki Shugaba Bola Tinubu, wanda ke zaune a wurin, ya tabbatar da kafa jihar Ibadan kafin shekarar 2027.

Wannan bukata ta basaraken na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Tarayya ke ci gaba da aikin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Bikin nadin Oba Ladoja ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na kasar nan ciki har da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Manyan jiga-jigai a Najeriya sun je Ibadan

Tsohon dan takarar shugaban kasa kuma jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan Jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Nadin Sarauta: Sarkin Musulmi ya isa Ibadan, ana dakon Tinubu da Atiku

Tun da farko, Afobaje na Ibadan, Cif Waheed Popoola, ya gudanar da al’adun gargajiya ta hanyar sanya ganyen Akoko a kan Oba Ladoja a gidan Labosinde, Oja’ba, in ji rahoton Daily Trust.

Daga nan kuma Sarkin ya wuce cikin jerin gwanon motoci zuwa Mapo Hall domin karbar sandar mulki daga gwamna da karisa wasu al'adu da aka shirya a bikin nadin.

Abokan Sarkin Ibadan sun halarci nadinsa

Daga cikin mahalarta bikin nadin Olubadan har da abokansa da ya yi aiki da su a siyasa irin su Sanata Sharafadeen Abiodun (Ibadan Kudu) da kuma tsohon ɗan takarar gwamnan Oyo, Teslim Folarin.

Sauran wadanda suka je wurin sun haɗa da Sanata Yunus Akintunde (Oyo ta Tsakiya), Sanata Abdulfatai Buhari (Oyo ta Arewa), da Olamijuwonlo Alao-Akala wanda ke wakiltar Ogbomoso ta Arewa a Majalisar Wakilai da sauran baki.

Olubadan na 44 ya hau karagar mulki a Oyo

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja ya zama Sarkin Ibadan a hukumance bayan karbar sandar mulki.

Rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da nadin sabon Sarkin a hukumance ne a bikin da ke gudana a jihar Oyo, ta Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Barau ya hango abin da mutanen Kano za su yi wa Tinubu a 2027

Gwamna Seyi Makinde ya mika sandar mulki ga sabon Sarkin Ibadan, Oba Ladoja, wanda ya kara tabbatar da nadinsa a matsayin Olubadan na 44.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262