Murna za Ta Koma Ciki: Sabon Rahoto Ya Cire Kano daga Ta 1 a Sakamakon NECO

Murna za Ta Koma Ciki: Sabon Rahoto Ya Cire Kano daga Ta 1 a Sakamakon NECO

  • Al'amarin nasarar Kano a jarrabawar NECO a kasar nan na shirin zama 'ta leko, ta koma' bayan an sake nazarin alkaluman da hukumar jarabawar ta fito
  • Da fari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ikirarin cewa jihar Kano ta samu matsayi na farko a sakamakon 2025 NECO-SSCE, inda ta doke jihohi irinsu Legas
  • Amma an ganowasu k alamai da hukumar NECO ta yi ne aka fassara ba daidai ba, amma jihar Kano tana mataki na karshe-karshe a jerin masu kokari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sababbin bayanai sun bulla a kan nasarar da gwamnatin Kano ta ke ikirarin daliban jihar sun samu a sakamakon NECO ta bana.

Da fari, Gwamna Abba Yusuf ya bayyana cewa jihar Kano ta fito daga cikin jihohin da su ka yi zarra wajen samun sakamako mafi kyau a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Gwamnatin katsina ta gano ma'aikatan bogi sama da 3,000

An sake bincike a kan sakamakon jarrabawar NECO
Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Binciken Premium Times ya bi bayanin da hukumar NECO ta fitar, inda ya karyata cewa Kano ce ta yi zarra a wajen samun sakamako mafi kyau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: An yi bincike kan sakamakon NECO

Daga bayanan da NECO ta fitar, daga cikin ɗalibai 1,358,339 da suka rubuta jarrabawar SSCE a 2025, 818,492 ne suka samu cin tarkardu biya, daga ciki ciki har da harshen Ingilishi da Lissafi.

Amma a cewar binciken, jihar Kano ta samu ɗalibai 68,159 amma hakan ba ya nufin cewa ita ce ke kan gaba a wajen wadanda su ka yi nasara ba.

Kano ta fi kowa adadin wadanda suka yi nasara, amma kasonsu ba shi ne a gaba ba.

Dangane da ƙididdigar wadanda su ka yi nasara, Kano ta na matsayi na 29 daga jihohi 37, inda ta kasance a rukunin jihohi goma da ke can karshe.

A cewar rahoton, Legas ta samu nasara fiye da Kano, inda kusan 71% na ɗalibai sun samu buƙatun sakamakon da ake bukata, yayin da Kano ta samu ƙasa da 50%.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa Gabdi ya ce gwamnoni ne matsalar kasar nan, ya ba talakawa shawara

Ina gwamnatin Kano ta samo bayaninta?

A cewar hukumar, 60.26% na ɗaliban da suka zauna jarabawar sun samu cin takardu biyar ko fiye, ciki har da darussan Turanci da Lissafi.

Shugaban NECO, Farfesa Ibrahim Dantani Wushishi, ya bayyana wa BBC cewa jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar.

Gwamna ya yi magana a kan NECO bayan kalaman shugaban hukumar
Hoton Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Farfesa Wushishi ya ƙara da cewa daga cikin ɗalibai 1,358,339 da suka zauna jarabawar bana, mutum 818,492 sun samu kiredit a aƙalla darussa biyar, ciki har da Lissafi da Turanci.

'Yan fursuna sun ci NECO a Kano

A baya, mun wallafa cewa Hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa wasu daga cikin daurarrun gidajen yari sun yi nasara a jarrabawar NECO.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, ta tabbatar da cewa fursunoni 68 ne suka yi nasara a jarabawar, abin da ta bayyana a matsayin wani babban cigaba a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Fursunoni a Kano sun yi jarrabawar NECO, kusan mutum 70 sun yi zarra

Hukumar ta ce wannan nasara ta zama abin alfahari ga fursunonin da suka amfana da damar, inda wasu daga cikinsu suka bayyana cewa hakan zai ba su damar gina rayuwarsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng