Bulama Bukarti Ya Hango Matsaloli a Sulhu da ƴan Ta'adda, Ya ba Gwamnati Shawara

Bulama Bukarti Ya Hango Matsaloli a Sulhu da ƴan Ta'adda, Ya ba Gwamnati Shawara

A cikin ‘yan watannin nan, ana iya ganin yadda ‘yan ta'adda ke kulla yarjejeniyar sulhu da mutanen garuruwa daban-daban, musamman a jihar Katsina.

A’isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware wajen kawo rahotanni kan al’amuran da suka shafi mata, yara da kuma siyasa.

Jihar Katsina – A cikin ‘yan kwanakin nan, ƙananan hukumomi kamar su Sabuwa da Matazu sun zauna da jagororin ‘yan ta'adda domin kawo karshen kashe-kashen bayin Allah da ake yi.

Bulama Bukarti ya yi tir da sulhu da yan ta'adda
Hoton fitaccen lauya Bulama BukartiHoto: @ZagazOlaMakama/Abdu Bulama Bukarti
Source: Facebook

Punch ta ruwaito a lokacin da ake irin wannan zama, ‘yan ta'addan da shugabanninsu ke wurin suna kai farmaki sassan Zamfara, tare da yi wa jama'a kisan gilla.

Wannan sulhu da ake yi, a cewar masanin shari’a kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, Bulama Bukarti, ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tattaunawar da ya yi da Legit, Barista Bulama Bukarti ya ce ba sulhu ake yi da ‘yan bindiga ba, mika wuya ake yi.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga ke koro mutane a Sakkwato, an tilasta wa jama'a hijira

Bulama: ‘Yan ta'adda na yi wa gwamnati barazana

A kalaman Bulama Bukarti, ya ce yanayin da ‘yan ta'adda ke fito da manyan bindigu da sauran mugayen makamai, hanya ce ta razana makiyansu da nuna ƙarfin iko.

Barista Bulama Bukarti ya ce:

"Fitowa da ‘yan bindiga suke yi da manya-manyan muggan makamai da sunan sulhu, su rika bagu suna alfahari da makaman nan, sun daure su a jikinsu, suna bayanai ana ɗauka a bidiyo da hotuna, kai tsaye da gangan suke yi don su tsoratar da mutane."
"Ai ta'addanci shi ne sanya wa mutane tsoro domin a cimma wata manufa da ake da ita ko ta siyasa, ko ta addini, ko ta kabilanci."
Bulama Bukarti ya ce yan ta'adda na bagu da makamai
Taswirar jihar Katsina, daya daga cikin jihohin da ke sulhu da yan ta'adda Hoto: @ZagaOlaMakama
Source: Original

Lauyan da ke fafutukar kare hakkin dan adam ya ce:

"Kuma da ka ga yadda mutanen nan suke fita da manyan mugayen makaman nan kamar za su je yaƙin duniya, to ka san da gangan suke yi domin su tsorata al’umma, domin su nuna wa gwamnatin Najeriya cewa babu abin da za ta iya yi."

Kara karanta wannan

An kama dilolin makamai a Nijar, an fara binciken 'yan siyasar Najeriya

"Tamkar ka ce irin atisayen da manyan makamai da dubunnan sojoji a ƙasashen duniya suke yi idan suna so su tsoratar da makiyansu, to haka su ma suke yi."

Bulama: Haramun ne ‘yan ta'adda su mallaki makamai

Barista Bulama Bukarti ya jaddada wa Legit cewa zaman da jama’a ke yi da ‘yan ta'adda, da yadda ‘yan bindiga suka mallaki makamai, ya saɓa da dokar ƙasa. A cewar fitaccen lauyan:

"Wannan abu kai tsaye haramun ne a dokokin Najeriya, haramun ne wani ya mallaki irin wannan makamai, kuma haramun ne wani ya fito yana yawo, yana tutiya, yana bagu da irin waɗannan makamai a dokokin Najeriya.
"Hatta zaman da ake cewa na sulhu ne tsakaninsu da al’ummar da suka daidaita, haramtaccen zama ne, domin babu dokar da ta ba da dama a yi irin wannan zama da sunan sulhu."

Barista Bulama Bukarti ya ƙara da cewa ba sulhu jama’a ke yi da ‘yan bindiga, mika wuya suke yi saboda sun fitar da rai cewa gwamnati ba za ta iya ceto su ba.

"An kashe su, an kashe su har an gaji. An sace su, an sace su har an gaji. An lalata masu dukiya, an daidaita su da gidajensu har sun gaji."

Kara karanta wannan

Matsala ta girma: An gano gawarwakin yan sanda 8 bayan sun bace a Najeriya

Ya ce jama’a suna nema wa kansu mafita ne saboda suna ganin kamar gwamnati ta kasa, kuma ba za ta iya takawa ‘yan ta'addan burki ba.

Shawarar Bulama Bukarti ga gwamnatin Najeriya

Ya ce yadda ‘yan ta'adda ke zuwa taron sulhu da mugayen makamai, kuma su koma dazuka da abinsu, ya tabbatar da cewa ba sulhu ake yi da gaske ba.

Bulama Bukarti ya shawarci gwamnati
Hoton Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bulama Bukarti ya ce:

"Sai ka ji suna cewa sun ba da dama mutane su je su yi noma. Duk wanda ya ba ka dama ka je ka yi noma, shi ke da iko da wurin da za ka je ka yi noman.
"Babu yadda za a yi mutumin gari wanda ba shi da bindiga, ya yi sulhu da ɗan bindiga mai mugayen makamai wai za a zauna lafiya. Ba sulhu ba ce, mika wuya ne."

Ya ce ‘yan bindiga yanzu sun zama kamar su ne gwamnati a wurin da suke cin karensu babu babbaka.

Ya shawarci gwamnatin tarayya ta tashi ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile ‘yan ta'addan marasa imani.

Fitaccen lauyan ya ce:

Kara karanta wannan

Tsohon dan bindiga mai shekara 70 da ya ajiye makamai ya yi jawabi a Katsina

"In kuma ba za ta iya ba, ita ya kamata ta shirya sulhu ko kuma mika wuya, amma a bi tsari mai kyau, a tabbatar kowa ya ajiye makamansa kuma an wanke kwakwalensu. Domin yanzu, ‘yan bindigan nan ba mutane ba ne, dodanni ne da suka dade suna shan jinin al’umma."

Kungiyoyi na damuwa da sulhun ƴan ta'adda

Kungiyar Centre for Legal Orientation and Humanitarian Aid Initiative (CELOHA NIGERIA) ta bayyana rashin amincewarta da tattaunawar sulhu da ƴan ta’adda.

Kungiyar ta shaida wa majiyar Legit cewa , zaman sulhu a jihohin Katsina da Zamfara, hanya ta gaza kawo dawwamammen zaman lafiya. A cewar M. Saeed Kano, wanda shi ne ya kafa CELOHA NIGERIA, duk da yawan tattaunawa da sulhun da ake yi, har yanzu hare-haren ba su tsaya ba.

Kungiyar ta nuna damuwarta cewa maimakon a samu sauƙi, mata da yara da kuma al’ummomi marasa laifi ne ke cigaba da fuskantar matsaloli.

Ta'addanci: Sheikh Gumi ya yi maraba da sulhu

A baya, mun wallafa cewa an samu gudanar da zaman sulhu tsakanin wasu shugabannin ‘yan ta’adda da wakilan kananan hukumomi biyu a Katsina.

Wakilan ƙananan hukumomin Sabuwa da Matazu ne suka halarci zaman tare da ‘yan ta’addan a yankunan da ake fama da hare-hare da garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

'A ina 'yan bindiga ke samun makami?' An yi wa Tinubu tambaya mai zafi

A Sabuwa, zaman ya gudana a kauyen Dugun Muazu, yayin da a Matazu aka gudanar da zaman ne a makarantar firamare ta Yargeza da ke Dan-Musa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng