An Cin Ma Yarjejeniya da Za Ta Kawo Saukin Kanjamau a Kasashe
- Mutanen da ke fama da cutar Kanjamau za su samu sauki wajen samun maganin da zai ba su kariya
- Hakan na zuwa ne baya an cin ma wata yarjejeniyar da za ta taimaka wajen samar da wata allura
- Allurar za a sayar da ita a kasashe masu karamin karfi a kan farashi mai araha sabanin kudin ta na $28,000
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
An cin ma yarjejeniyar samar da allurar Lenacapavir, wadda ake amfani da ita wajen hana kamuwa da cutar HIV.
Allurar za ta kasance mai araha a sama da kasashe masu karamin karfi fiye da 100 cikin shekara biyu masu zuwa.

Source: Twitter
Tashar BBC ta ce wannan mataki na zuwa ne bayan kulla yarjejeniya ta tarihi tsakanin kungiyar Clinton Health Access Initiative (CHAI) da sauran kungiyoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran kungiyoyin da aka kulla yarjejeniyar da su sun hada Dr. Reddy’s Laboratories, Unitaid, Gates Foundation, Wits RHI, da sauran abokan hulɗa.
Za a samar da allura don yakar Kanjamau
Yarjejeniyar za ta ba Dr. Reddy’s Laboratories tallafin kuɗi, fasaha, domin su samar da ingantacciyar allurar Lenacapavir.
Allurar za a samar mata lasisin sayarwa a kasashe masu karamin karfin tattalin arziki nan da shekarar 2027 bayan izinin hukumomin lafiya.
A gwaje-gwajen asibiti, an gano cewa Lenacapavir tana rage haɗarin kamuwa da cutar HIV sosai har ma ya kai ga kusan cikakkiyar kariya ga masu amfani da ita.
Ingancin allurar ya fi na tsofaffin magungunan da ake amfani da su a matsayin PrEP, wato magungunan hana kamuwa da cutar.
Abin sha’awa, ana yin allurar ne sau biyu, kuma za a fara samar da ita a karshen wannan shekara a farashin Dala 28,000 kan kowanne mutum a shekara.
Sai dai sanarwar da aka yi a ranar Laraba ta tabbatar da cewa sabon shirin zai rage wannan farashi zuwa Dala 40 kacal, wanda ya kai kusan kaso 0.1% na farashin allurar.
Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton, wanda shi ne shugaban kwamitin gudanarwa kuma wanda ya kafa CHAI, ya yaba da shirin.
Bill Clinton ya bayyana cewa damar da ake da ita na kare lafiyar mutum tsawon watanni shida da allura guda ɗaya a farashin da bai wuce na kwayoyin da ake sha kullum ba, abu ne da ya sauya tarihi matuka.

Source: Twitter
Hukumar NACA ta yaba da matakin
Jaridar TheCable ta ce shugabar hukumar kula da cutar kanjamau ta kasa (NACA), Dr Temitope Ilori, ta ce wannan sabuwar hanya ta hana kamuwa da cutar HIV abin a yaba ce.
Ta bayyana cewa zabin amfani da allurar zai bayar da kariya mai tsawo, saukin amfani, da kuma ingantacciyar mafita ga miliyoyin mutane da ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
Ta kara da cewa wannan yarjejeniyar ta buɗe kofar samun damar amfani da Lenacapavir cikin araha, wanda zai taimaka wajen rage yaduwar cutar HIV a Najeriya da duniya baki daya.
Najeriya ta ware kudi don yakar Kanjamau
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar zartaswa ta tarayya (FEC), ta amince da sayen magunguna don yakar cutar HIV.
Majalisar ta amince da ware Naira biliyan 4.5 don sayen magunguna domin tallafawa 'yan Najeriya masu dauke da cutar Kanjamau.
Amincewar na zuwa ne bayan matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na soke dakatar da tallafin kula da masu HIV a kasashe masu tasowa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


