Tarihin cutar Kanjamau a takaice

Tarihin cutar Kanjamau a takaice

Cutar Kanjamau mai karya garkuwar jiki cuta ce da a turance ake kiranta AIDS (Acquired Immune Deficiency Syndrome) wanda ake samun ta daga kwayoyin cuta na HIV (Human Immunodeficiency Virus).

Kamar yadda wani malami na jami'ar Quinnipiac ta birnin Connecticut dake kasar Amurka ya bayyana, Farfesa William ya ce ko shakka ba bu ba za mu san ta yaya ko yadda aka yi ba cutar ta samo asali sai dai kawai a ci gaba da hasashe.

Tarihi na asalin cutar kanjamau yana tattare da kurdada ta tufka da warwara tun gabannin shekarar 1980, inda cikin gayya wani ma'aikacin cikin jirgi na kasar Canada, Gaetan Dugas, ya ke goga cutar ga kimanin mutane 250 a kowace shekara, sai dai mutane da dama sun yi watsi da wannan kauli na tarihi.

Kwayoyin Cutar Kanjamau
Kwayoyin Cutar Kanjamau

A Wani binciken na'ura mai kwakwalwa watau Computer Models da aka gudanar ya bayyana cewa, cutar kanjamau ta bayyana tun gabanin shekarar 1930.

Wani binciken ya kuma bayyana cewa, cutar kanjamau ta fara bayyana ne a jikin dan Adam a shekarar 1959, bayan da kwararrun kiwon lafiya suka bankado tare da tabbatar da ita a jikin wani mutum dan kasar Jamhuriyyar Congo.

KARANTA KUMA: Jerin Jihohi 11 mafi yawan masu cutar Kanjamau a Najeriya

Rahotanni daga kasar Andalus sun kuma bayyana cewa, dan Adam ne ya hada wannan cuta ta kanjamau a dakin bincike da gwaje-gwaje dake tsuburin Plum daura da kasar Amurka, inda mayakan kasar Jamus suka nufaci amfani da ita a matsayin makami a yayin yakin duniya na biyu.

Legit.ng ta kuma kawo muku rahoton cewa, wata mata 'yar kasar Saudiya ta shafe tsawon shekaru 25 ta na jinyar mijinta ba tare da kosawa ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng